Yanzu Yanzu: Matasan Arewa sun jero kura-kurai 6 a gudanarwar zaben Shugaban kasa na 2019

Yanzu Yanzu: Matasan Arewa sun jero kura-kurai 6 a gudanarwar zaben Shugaban kasa na 2019

Kungiyar matasan Arewa ta caccaki hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki kan gudanarwar zaben 2019.

A wani sanarwa daga Shugaban kungiyar, Alhaji Yerima Shettima, ya lissafa wasu kura-kurai 6 akan jam’iyya mai mulki da jami’an zabe.

Kungiyar Arewar ta bayyana cewa: “Mun lura cike da dacin rai yadda aka gudanar da zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokoki sannan muna fatan nuna rashin jin dadi da hukumar INEC da APC kan yadda suka hada kai.

Yanzu Yanzu: Matasan Arewa sun jero kura-kurai 6 a gudanarwar zaben Shugaban kasa na 2019
Yanzu Yanzu: Matasan Arewa sun jero kura-kurai 6 a gudanarwar zaben Shugaban kasa na 2019
Asali: Facebook

Sannan muna burin lissafo su kamar haka:

1. Cewa INEC, don yin alfarma ga jam’iyyar APC mai mulki ta daga zabe da gangan domin ba jami’iyya mai mulki damar yin magudi.

2. Cewa anyi amfani da yan iska wajen zabe, musamman a wasu jihohin kudu, domin ba jam’iyya mai mulki dammar yin abunda ta ga dama da takardun sakamakon zabe.

3. Cewa a yankunan arewacin kasar, imam an jirkirta zabe ko kuma an lauya jerin sunayen masu zabe domin alfarma ga APC. Hakan bai dace ga zabe na gaskiya da amana ba.

KU KARANTA KUMA: Hukumar INEC na cikin ganawa don sake duba zaben shugaban kasa

4. Cewa an razana masu zabe da ban a jam’iyya mai mulki bane bayanj jami’an jam’iyya mai mulki sun hada kai da jami’an zabe.

5. Da kusan kaso 90% jerin sunayen masu zabe da aka yiwa rijista ya sauka sosai da adadin wadanda suka kada kuri’a a fadin kasar.

6. Cewa akwai cece-kuce sosai a kokarin magance barazana da tozarcin da aka yiwa masu zabe a kusan dukkanin mazabu a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel