Dodar-ta-tabbata: Rarara ya saki sabuwar wakar nasarar Buhari a zaben 2019 (Bidiyo)

Dodar-ta-tabbata: Rarara ya saki sabuwar wakar nasarar Buhari a zaben 2019 (Bidiyo)

Fitaccen mawakin nan a masana'antar nishadantarwar Hausa da Kannywood na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) watau Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya saki sabuwar waka biyo bayan nasarar da shugaba Buhari ya samu a zaben ranar Asabar.

Wakar dai wadda muka samu labarin cewa ya rera ta ne tare da taimakon aminin nan nasa watau Babaan Chinedu ya sake ta ne yau awoyi kadan bayan kammala bayyana sakamakon saben da shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu yayi.

Dodar-ta-tabbata: Rarara ya saki sabuwar wakar nasarar Buhari a zaben 2019 (Bidiyo)
Dodar-ta-tabbata: Rarara ya saki sabuwar wakar nasarar Buhari a zaben 2019 (Bidiyo)
Asali: UGC

KU KARANTA: Cikakken sakamakon zaben shugaban kasa jiha-bayan-jiha

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa fitar wakar ke da wuya tuni har ta soma karade dukkan fadin kasar musamman ma arewacin ta da kuma inda ke da Hausawa yayin da tuni masoyan APC din suka fara kunna ta a cikin manyan motocin kamfen suna murna.

Shi dai Dauda Rarara ya shahara sosai wajen fagen wakoki musamman na Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki kuma a lokuta da dama yakan yi waka domin nuna goyon bayan sa.

Haka nan ma dai mawakin yana da matukar farin jini a tsakanin masoyan jam'iyyar ta APC inda a lokuta da dama sukan ji wakokin sa saboda su samu kwarin gwuiwa da karsashi a wuraren siyasa da taruka.

Ga dai bidiyon wakar nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng