Tunda nike a rayuwata, ban taba shan kwaya ba - CP Wakili

Tunda nike a rayuwata, ban taba shan kwaya ba - CP Wakili

- Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, Mohammed Wakili, ya karyata jita-jitar da ke yawo na cewar shi kasurgumin dan shaye shaye ne

- Mr Wakili ya ce haka Allah ya halicce shi; yin magana kamar wanda ya bugu, da kuma kakkarya sassan jikinsa idan yana furuci

- A cewar sa: "Idan da ace gaba daya hukumomin tsaro za su taru a yaki shan kwaya, to kuwa za mu iya kawo gagarumin canji."

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kano, Mohammed Wakili, wanda aka fi sani da 'Maza Kwaya - Mata Kwaya', ya karyata jita-jitar da ke yawo na cewar shi kasurgumin dan shaye shaye ne, yana mai cewa: "Tunda nike a rayuwata, ban taba shan kwaya ba."

Da ya ke zantawa da jaridar Daily Trust ta ranar Asabar, Mr Wakili ya ce haka Allah ya halicce shi; yin magana kamar wanda ya bugu, da kuma kakkarya sassan jikinsa idan yana furuci, wanda da yawan jama'a ke kallo a matsayin buguwa daga shan kwaya ko kayan maye.

"Wata kila lura da yadda nake furuci ko karya gabobin jikina, wasu ke kallo a matsayin kamar dan shaye shaye, amma haka Allah ya halicce ni. Ina yin magana kamar wanda ya bugu da kwaya, sannan nakan yi amfani da gabban jikina wajen yin furuci, wanda da yawa ke kallo a matsayin abun ban dariya, ko kuma alamar dan kwaya, amma hakan halittata ta ke.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Jami'in tattara sakamakon zabe ya yi yunkurin guduwa, an cafke shi

Tunda nike a rayuwata, ban taba shan kwaya ba - CP Wakili
Tunda nike a rayuwata, ban taba shan kwaya ba - CP Wakili
Asali: UGC

"Ni haka Allah ya yi ni, kuma babu wani abu da zan iya yi akan hakan. Ban taba shan kwaya ba a rayuta, kuma har sai da na shiga aikin dan sanda ne na san sunayen wasu kwayoyin," a cewar sa.

Mr Wakili ya jaddada cewa zai ci gaba da yakar shaye shaye musamman kwaya har sai na ga abunda ya turewa Buzu nadi, yana mai cewa: "Haka kawai na ke jin sha'awar sadaukar da rayuwata, karfina, iko na wajen ganin an kawo karshen shan kwaya saboda na fahimci illar da ke tattare da shan kwayar.

"Gaskiya ba zan iya tsayawa ina kallo shaye shaye na ci gaba da lalata rayuwar al'ummarmu in yi shiru ba, musamman a yanzu da na ke da wani iko na ganin an dakile shan kwaya, ko da ba zan iya magance hakan gaba daya ba, amma zan bayar da iyakar iyawata."

A cewar sa: "Idan da ace gaba daya hukumomin tsaro za su taru a yaki shan kwaya, to kuwa za mu iya kawo gagarumin canji."

Mr Wakili, ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki, musamman hukumomin NDLEA, NAFDAC, da kuma hukumar shige da fice da ma sauran hukumomin tsaro da su kasance masu gudanar da ayyukansu kamar yadda ya dace.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel