Zaben Shugaban kasa: Atiku na gaba da Buhari a Benue inda ya lashe 7 daga cikin kananan hukumomi 11

Zaben Shugaban kasa: Atiku na gaba da Buhari a Benue inda ya lashe 7 daga cikin kananan hukumomi 11

- Dan takarar Shugaban kasa a jam’ iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, na kan gaba a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar a jihar Benue

- Atiku ya lashe kananan hukumomi bakwai cikin 11 da ke jihar yayinda Buhari ya lashe hudu

- A yanzu haka ana jiran sakamako na sauran kananan hukumomi 12

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, kuma dan takarar Shugaban kasa a jam’ iyyar Peoples Democratic Party (PDP), na kan gaba a zaben Shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar a jihar Benue.

A yanzu ya lashe kananan hukumomi bakwai cikin 11 da ke jihar.

Zaben Shugaban kasa: Atiku na gaba da Buhari a Benue inda ya lashe 7 daga cikin kananan hukumomi 17
Zaben Shugaban kasa: Atiku na gaba da Buhari a Benue inda ya lashe 7 daga cikin kananan hukumomi 17
Asali: UGC

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rahoto a ranar Litinin, 25 ga watan Fabrairu cewa har yanzu ana kan harhada sakamakon zabe a fadin jihar, inda Atiku ke jagoranci a kananan hukumomin Gwer West, Buruku, Logo, Agatu, Apa, Ado, da kuma Obi.

Sakamakon ya nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a baya a kananan hukumomi hudu.

Zuwa yanzu dai Buhari ya lashe Tarka, Ushongo, Konshisha da kuma Ohimini yayinda ake jiran sakamako daga sauran kananan hukumomi 12.

KU KARANTA KUMA: Saraki: PDP tayi watsi da sakamakon zaben Kwara ta tsakiya

Kananan hukumomin da ake jira sune Gboko, Guma, Makurdi, Katsina, Vandeikya, Otukpo, Ogbadibo, Oju, Kwande, Gwer East, Ukum da kuma Guma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel