Da duminsa: PDP ta lallasa APC a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, Bauchi

Da duminsa: PDP ta lallasa APC a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, Bauchi

Rahotan da muke samu yanzu na nuni da cewa jam'iyyar PDP mai mulki a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi, ta samu gagarumar nasara akan jam'iyyar APC, da tazarar kuri'u 20670.

Mazabar ce kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara ke wakilata a majalisar wakilan tarayyar, inda kuma yake neman tazarce a karo na hudu, karkashin jam'iyyar PDP.

Bisa rahotannin da muka samu, jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 72, 334 yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 51, 664.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Sakamakon zabe daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Da duminsa: PDP ta lallasa APC a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, Bauchi
Da duminsa: PDP ta lallasa APC a mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, Bauchi
Asali: Twitter

Sai dai, Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa, Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC na ci gaba da sake gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya a rumfunan zabe na garin Kofti, mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa, jihar Bauchi, sakamakon lalacewar na'urar tantance masu kad'a kuri'a.

A halin yanzu, kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, shi ke wakiltar mazabar a majalisar wakilan tarayya, wanda kuma ke neman tazarce a karo na hudu, karkashina jam'iyyar PDP.

A cewar jami'an INEC da ke cibiyar tattara kuri'un mazabar da ke garin Zwall, an sake gudanar da zaben ne na rumfar zaben garin Kofti, bayan da na'urorin tantance masu zabe suka gaza yin aiki har bayan karfe 2 na ranar Asabar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel