Yanzu yanzu: Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya sha kasa a karamar hukumar Kwami

Yanzu yanzu: Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya sha kasa a karamar hukumar Kwami

- Dan takarar APC a mazabar Gombe ta Arewa ya lallasa na jam'iyyar PDP a karamar hukumar Kwami

- Sanata Alkali ya samu kuri'u 26, 795 yayin da Dankwambo ya samu kuri'u 14,019

- Karamar hukumar kwami na daya daga cikin kananan hukumomi biyar na mazabar majalisar dattijan

Dan takarar kujerar mazabar Gombe ta Arewa a majalisar dattijai, Sanata Saidu Ahmed Alkali ya lashe zaben karamar hukumar Kwami da ke jihar Gombe.

Ya lallasa babban abokin hamayuarsa, Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda shi ne gwamnan jihar mai ci a yanzu, da ke takara karkashin jam'iyyar PDP.

KARANTA WANNAN:

Yanzu yanzu: Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya sha kasa a karamar hukumar Kwami
Yanzu yanzu: Gwamna Dankwambo na jihar Gombe ya sha kasa a karamar hukumar Kwami
Asali: Depositphotos

Bisa rahotanni na sakamakon da aka wallafa na gundumomi 10 da ke karamar hukumar, Sanata Alkali na jam'iyyar APC ya samu kuri'u 26, 795 yayin da Dankwambo ya samu kuri'u 14,019.

Karamar hukumar kwami na daya daga cikin kananan hukumomi biyar na mazabar majalisar dattijan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel