Da duminsa: Yadda Yakubu Dogara ya kawowa Atiku kuri'ar akwatin zabensa

Da duminsa: Yadda Yakubu Dogara ya kawowa Atiku kuri'ar akwatin zabensa

- Yakubu Dogra, ya kawowa Alhaji Atiku Abubakar kuri'ar akwatin da ya kad'a zabensa, a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da ya gudana a ranar Asabar

- A akwatin zaben Dogara mai lamba 007A, jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 285 yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 15, yayin da kuri'u 19 suka lalace

- Haka zalika, a wani akwatin zabe da ke cikin kauyen kakakin majalisar wakilan tarayyar, PDP ta samu kuri'u 290 yayin da APC ta samu kuri'u 9

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogra, ya kawowa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar kuri'ar akwatin da ya kad'a zabensa, a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya da ya gudana a ranar Asabar.

Yakubu Dogara, wanda a baya bayan nan ya sauya sheka daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar adawa ta PDP, ya kad'a kuri'arsa a akwatin zabe na makarantar firamaren Gwaranga a karamar hukumar Bogoro, jihar Bauchi, inda ya ke neman tazarce a karo na hudu domin wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa.

Ya kad'a kuri'arsa da misalin karfe 9:45 na safiyar ranar Asabar.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Sakamakon zabe daga jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Da duminsa: Yadda Yakubu Dogara ya kawowa Atiku kuri'ar akwatin zabensa
Da duminsa: Yadda Yakubu Dogara ya kawowa Atiku kuri'ar akwatin zabensa
Asali: Twitter

A akwatin zaben Dogara mai lamba 007A, jam'iyyar PDP ta samu kuri'u 285 yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 15, yayin da kuri'u 19 suka lalace.

A wani akwatin da ke cikin kauyen Dogara da ke cikin babbar makarantar Firamare ta Gwarangah, Bauchi, mai lamba 007B, PDP ta samu kuri'u 265 yayin da APC ta samu kuri'u 16, inda kuri'u 18 suka lalace.

Haka zalika, a wani akwatin zabe da ke cikin kauyen kakakin majalisar wakilan tarayyar, PDP ta samu kuri'u 290 yayin da APC ta samu kuri'u 9.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel