KAI TSAYE: APC ta sha kasa a kujerar Sanatan Katsina ta Arewa, rumfar zaben Buhari

KAI TSAYE: APC ta sha kasa a kujerar Sanatan Katsina ta Arewa, rumfar zaben Buhari

SHIMFIDA: A yayin da aka kammala kad'a kuri'u a wasu sassa na jihohi 36 na kasar Nigeria, ciki kuwa har da jihohin Bauchi, Gombe da Filato, tuni aka fara tattara kuri'u tare da kidaya su a wasu rumfunan zabe na jihohin. Sai dai har zuwa yanzu akwai rumfunan zaben da ba su kammala kad'a kuri'arsu ba.

Legit.ng Hausa ta shirya kawo maka labarai kai tsaye, dangane da tattara kuri'u da kuma kidayarsu a jihohin Bauchi, Gombe da Filato, domin baka damar sanin halin da zaben jihohin ya ke ciki.

HATTARA: Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ce kadai ke da ikon tattara kuri'u da fadin sakamakon zabe. Bayanai kan sakamakon kuri'un da aka kad'a a mazabun da zaka karanta a wannan shafin ba daga hukumar INEC ya ke ba. Legit.ng Hausa ba za ta iya tantance gaskiyar sakamakon ba.

KARANTA WANNAN: KAI TSAYE: Yadda zabe ke gudana a jihohin Bauchi, Gombe da Filato

Duba yadda ake ci gaba da tattara sakamakon zabe da kidaya a wasu sassa na kasar...

4:00pm-5:00pm:

Rahotan da muke samu na nuni da cewa dan takarar sanatan mazabar Katsina ta Arewa karkashin jam'iyyar APC, Ahmad Baba Kaita ya sha kasa a rumfar zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke gundumar Sarkin Yara (A), Kofa Baru (3), Gidan Niyam da ke karamar hukumar Daura, jihar Katsina.

Jam'iyyar Accord ce ta lashe zaben.

Jami'in hukumar zabe mai kula da rumfar, Aliyu Abdullahi ya sanar da cewa dan takarar na APC, Ahmad Baba Kaita, ya samu kuri'u 247, Mani Nasarawa (PDP) ya samu kuri'u 2 yayin da Mohammed Lawal Nalado na jam'iyyar Accord ya samu kuri'u 262.

Sai dai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe zabensa a rumfar zaben, inda ya samu kuri'u 523, yayin da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 3 kacal.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel