Yanzu Yanzu: Gaidam na karkashin harin Boko Haram

Yanzu Yanzu: Gaidam na karkashin harin Boko Haram

Kasa da sa’a guda kafin fara zaben Shugaban kasa da na yan majalisar dokokin kasar, a yanzu haka garin Gaidan a jihar Yobe na karkashin harin Boko Haram.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gano maharan a Maladari, wani kauye da ke kilomita 6 zuwa Gaidam da misalin karfe 3:00 na tsakar dare.

“Sun iso garin Gaidam da misalin karfe 6:15 na safe sannan suka fara harbi ba kakkautawa.”

“Mazauna yankin harda shugabanni na tserewa daga garin. A yanzu haka da nake Magana ina gudun hijira a Bukarti, kauyen gwamnan jihar amma an fada mana cewa maharani na hanyarsu ta zuwa,” inji wani mazaunin yankin da ya ambaci sunansa a matsayin Muhammad.

Yanzu Yanzu: Gaidam na karkashin harin Boko Haram

Yanzu Yanzu: Gaidam na karkashin harin Boko Haram
Source: UGC

Ya bayyana cewa mazauna yankin da dama sun tsere daga garin zuwa daji tare da matayensu da yara ba tare da sanin inda suka nufa ba. “Muna cikin wani yanayi na wahala, bamu san abun yi ba,” inji shi.

Garin Gaidam ya fuskanci hare-hare da dama daga yan ta’addan Boko Haram inda yayi sanadiyar mutuwar sojoji da yan ta’adda da dama.

KU KARANTA KUMA: Kai tsaye: Yadda zaben Shugaban kasa da na yan majalisa ke gudana a jihohin Niger, Kwara da Nasarawa

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa Mazauna garin Maidguri, babban birnin jihar Borno sun shiga cikin dar da safen nan inda suka waye gari da tashi bama'bamai cikin mintuna goma.

Bama-bamai 7 sun tashi tsakanin karfe 5:50 da 6:00 na asuban nan A yanzu haka ana jin harbe-harbe a cikin birnin Maidugurin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel