Bauchi 2019: Yadda aka rarraba kayan zabe a kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi

Bauchi 2019: Yadda aka rarraba kayan zabe a kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi

- Rahotannin da Legit.ng Hausa ta tattara, na nuni da cewa na kammala rarraba kayayyakin zabe a kananan hukumomi ashirin na jihar Bauchi

- Rabon kyayyakin wanda ya gudana a babban bankin Nigeria reshen jihar, ya gudana ne karkashin sa idon jami'an tsaro da kuma jami'an jam'iyyun siyasa

-Shugaban sashen ilimantar da masu zabe a hukumar INEC, Ahmed Waziri ya ce an dauki matakan tsaro domin gudanar da sahihin zabe a jihar

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta tattara, na nuni da cewa na kammala rarraba kayayyakin zabe da suka hada da takardun kad'a kuri'a, takardun rubuta sakamako da kuma na'urar tantance masu zabe a kananan hukumomi ashirin na jihar Bauchi.

Rabon kyayyakin wanda ya gudana a babban bankin Nigeria reshen jihar, ya gudana ne karkashin sa idon jami'an tsaro da kuma jami'an jam'iyyun siyasa, inda suka raka kayyakin har zuwa kananan hukumomin domin raba su ga rumfunan zabe.

Wakilin Legit.ng Hausa a jihar ta Bauchi, Sani Hamza Funtua, wanda ya halarci wajen rabon kayayyakin a ranar Litinin, ya ruwaito cewa sabanin zabukan baya, wannan karon an dakatar da 'yan jaridu daga shiga cikin harabar babban bankin, inda aka gudanar da rabon kayayyakin.

KARANTA WANNAN: Saboda Buhari, zan iya rike mukamin shugaban karamar hukuma - Tsohon gwamnan Bauchi

Bauchi 2019: Yadda aka rarraba kayan zabe a kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi
Bauchi 2019: Yadda aka rarraba kayan zabe a kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi
Source: UGC

Wasu na kallon rabon muhimman kayayyakin zaben ana saura kwanaki biyu kafin gudanar da zaben, a matsayin wani lamari mai sanya shakku, wanda jama'a da dama ke wasi-wasin yadda za a killace kayan a wannan lokaci ba tare da wata barazana ba.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a mashigar bankin, shugaban sashen ilimantar da masu zabe a hukumar INEC, Ahmed Waziri ya ce an dauki matakan tsaro domin ganin cewa an gudanar da sahihin zabe a jihar.

Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa kananan hukumomi masu nisa kamar Zaki, Gamawa da Jama'are su ne a sahun farko da aka fara raba masu kayayyakin zaben.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel