Yan Najeriya zan saida wa NNPC ba abokai na ba - Atiku

Yan Najeriya zan saida wa NNPC ba abokai na ba - Atiku

Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP), Atiku Abubakar ya bayyana cewa yan Najeriya zai saida wa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) idan har aka zabe shi a matsayin Shugaban kasa.

Atiku ya yi watsi da rahotannin cewa yana da niyan siyar da NNPC ne ga iyalansa sa kuma abokansa.

Dan akarar Shugaban kasa ya fayyace gaskiyar ne a lokacin ganawa da shugabanni a jihar Kaduna.

Yan Najeriya zan saida wa NNPC ba abokai na ba - Atiku

Yan Najeriya zan saida wa NNPC ba abokai na ba - Atiku
Source: Twitter

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa lallai zai siyar wa dya Najeriya da hukumar ne domin ci gaban kasar.

“Suna ta cewa Atiku na so ya siyarwa da kanshi da abokansa NNPC. Wannan karya ne!

“Ba su so mu siyar da NNPC amma sai mun siyar da shi. Zamu siyar maku da shi. Za ku sya? Ya tambaya."

Tambayar tasa ta sa mutane na ta ihun ‘Eh’.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Hukumar yan sanda ta sauya kwamishinoni a Adamawa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Atiku Abubakar ya yi kira ga 'yan Najeriya su fito kwansu da kwarkwata a ranar Asabar su kayar da shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari kamar yadda suka kayar da Shugaba Goodluck Jonathan a ranar 28 ga watan Maris na 2015.

Atiku ya yi wannan furucin ne a cikin sakon da ya fitar a faifan bidiyo a shafinsa na Twitter. Tsohon mataimakin shugaban kasa ya ce ranar zabe rana ce da dukkan 'yan Najeriya suke da 'yanci iri daya saboda kowa kuri'a daya ya ke da ita.

Ya bukaci 'yan Najeriya suyi zabe a kan kasancewa da cigaba da rayuwarsu kamar yadda ta ke a cikin shekaru hudu da suka gabata ko kuma su nemi sauya rayuwarsu da abin da yafi alheri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel