Da duminsa: Da ku zabi dan Izalah, gwara ku zabi Kirista - Sheik Dahiru Bauchi ya yi kira ga jama'a su zabi Yakubu Dogara

Da duminsa: Da ku zabi dan Izalah, gwara ku zabi Kirista - Sheik Dahiru Bauchi ya yi kira ga jama'a su zabi Yakubu Dogara

Shahrarren malamin addinin Musulunci kuma shugaba Darikatul Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga mutanen yankin Bogoro/Dass/da Tafawa Balewa a jihar Bauchi da su zabi kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara.

Ya bayyana hakan ne yayinda kakakin ya kaiwa babban malamin ziyara gidansa inda yayi kira ga jama'a kada su zabi malaman da amfani da addini wajen raba kan al'umma.

Ya ce Yakubu Dogara bai nuna bangarancin addini, yana son zaman lafiya, kuma ya cancanci ya wakilci jama'a domin cigaba da ayyukan kwarai da yakeyi.

Ya kara da cewa Yakubu Dogara ya yi ayyukan a zo a gani ga mutanen jihar Bauchi da yankin Arewa maso gabas gaba daya, saboda haka, jama'a su mayar masa da alkhairi ta hanyar zabensa ranan Asabar.

KU KARANTA; Ban yi murabus ba - Osinbajo ya karyata rahotanni

Yace: "Gwanda a zabi Kirista da dan Izalah wanda bai ganin mutuncin yan darika." Izalah da Darika duk Musulmai ne, amma wanda ake son ya ci zaben mutumine wanda ya shahara wajen zagin manyan malamansu, yayyinmu, kuma yana ikirarin shi Musulmi ne.

Wannan kaman suka ne ga mahaifina, mahaifiyata, malamaina kuma ba zamu taba goyon bayan irin wannan mutum ba."

Ya yiwa Yakubu Dogara addu'an nasara a zabe mai zuwa da kuma cigaban zaman lafiya a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel