Kallabi tsakanin rawuna: Ku sadu da CSP Nana Bature Garba, wata jarumar 'yar sanda daga Arewa

Kallabi tsakanin rawuna: Ku sadu da CSP Nana Bature Garba, wata jarumar 'yar sanda daga Arewa

A cigaba da kawo maku hazikai kuma fitattun mutane daga Arewacin Najeriya da suke tattare a ababen koyi ko kuma wata fasahar da zata iya anfanuwar mu baki daya, yau mun kawo maku wata tauraruwarmu mai suna CSP Nana Bature Garba, wata DPO din ‘yan sanda a Abuja.

A bisa al'adar mu dai mafi yawanci aikin damara a Arewacin Najeriya an fi alakanta shi ne da maza don kuwa ba kasafai ne mata ke nuna sha'awar su ta shiga irin ayyukan ba saboda yadda ake yi masu kallo.

Kallabi tsakanin rawuna: Ku sadu da CSP Nana Bature Garba, wata jarumar 'yar sanda daga Arewa

Kallabi tsakanin rawuna: Ku sadu da CSP Nana Bature Garba, wata jarumar 'yar sanda daga Arewa
Source: Facebook

KU KARANTA: Yan bindiga sun kashe soja 1 a Katsina

Sai dai ita wannan jarumar matar, ta bayyana cewa tana matukar sha'awar aikin da take yi kuma ma hasali ita ce ta nemi aikin duk kuwa da irin turjiyar da ta dan samu daga 'yan uwa da abokai kafin ta fara.

Da kuma take bayanin irin kalubalen da ta fuskanta a aikin nata, CSP Nana Bature tace ba zata taba mantawa da yadda wasu barayi suka galabaitar da ita da sauran ‘yan sanda yayin da suka je kama kayan sata, amma hakan bai sa ta karaya ba.

Ta cigaba da cewa kafin nan an gargade ta cewa kar ta sake ta shiga kasuwar Panteka da ke unguwar Mpape a Abuja, saboda hadarin da za ta iya fuskanta daga barayin zaune.

Ta ce barayin sun galabaitar da su, amma daga baya ta cimma burinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel