Zabe: Akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano – Kungiyar masu sa ido a zabe

Zabe: Akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano – Kungiyar masu sa ido a zabe

Kungiyar hada kuri’u ta INEC ta tantance masu sa ido a zabe a Jihar Kano, sun kuma tabbatarwa yan uwansu da cewa akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya a jihar.

Shugaban kungiyar, Kwamrad Friday Maduka, yayi kiran ne yayinda yake jawabi a taron manema labarai a Kano a ranar Laraba, 20 ga watan Fabrairu.

A cewar shugaban kungiyar, hukumar Zabe na kasa (INEC) ta kammala shirye-shirye akan yanda zata kamanta gaskiya da kuma jajircewa wajen gudanar da zabe mai cike da gaskiya kamar yanda ta samarwa jam’iyyun siyasa filin wasa a fagen siyasa don kada kuri’u.

Zabe: Akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano – Kungiyar masu sa ido a zabe

Zabe: Akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano – Kungiyar masu sa ido a zabe
Source: Facebook

Har ila yau dai, yayi kira ga hukumomin tsaro, musamman yan sanda, da su karfafa kokarinsu wajen magance yan bangan siyasa don inganta kwanciyar hankali da zaman lafiya tsakanin al’umma a jihar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Na hannun daman Buhari da wasu da dama sun koma jam’iyyar PDP

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yayi jawabi mai kaushi game da yakin neman zaben 2019. Tsohon gwamnan na Kano yayi magana a kan wadanda ke rusa fastocin ‘yan takarar PDP a kano.

Rabiu Kwankwaso yake cewa wasu matasa da ake ba kayan shaye-shaye, sun zo har gaban gidan sa, sun yi fata-fata da alamomin Atiku Abubakar da ya makala. Kwankwaso ya bayyanawa wasu ‘yan jarida wannan ne a gidan sa.

Kwankwaso yace wadannan mutane da su ka yi masa irin wannan ta’adi sun taki sa’a cewa ba ya nan, inda yace da a ce yana gida lokacin da aka yi wannan aiki, da ya nemi a dirkawa wadannan mutane dalma a jikinsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel