Allah-kare-bala'i: 'Yan bindiga sun kashe babban jami'in soja da farar hula 6 a Katsina

Allah-kare-bala'i: 'Yan bindiga sun kashe babban jami'in soja da farar hula 6 a Katsina

Wasu ‘yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun kai farmaki a wani tare da kashe mutane akalla 7 da kuma jikkata wasu da dama, cikin har da wani babban jami'in rundunar soja kaftin na sojoji a wasu hare-hare da suka kai a wasu kauyukan jahar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kuma yi awan gaba da daruruwan dabobi a kauyen Kasai da ke karamar hukumar Batsari.

Allah-kare-bala'i: 'Yan bindiga sun kashe babban jami'in soja da farar hula 6 a Katsina

Allah-kare-bala'i: 'Yan bindiga sun kashe babban jami'in soja da farar hula 6 a Katsina
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Atiku ma ya san bai iya kada Buhari - Oshiomhole

Jaridar This Day ta rahoto yadda ‘yan ta’addan suka aukawa kauyen da misalin karfe 1:00 na dare inda suka yi ta harbe-harbe, lamarin da ya sa mazaune kauyen suka yi ta tserewa.

Sun kai hari sansanin sojojin da ke garin inda suka harbe kaftin din sannan suka kona motar sintirin sojojin. Daga bisani, an yi barin wuta tsakanin sojoji da ‘yan bindigar.

Shugaban karamar hukumar Batsari, Mannir Mu’azu Rumah ya ce adadin ‘yan bindigar ya kai kimanin dari. Ya ce banda dabobi, sun yi awan gaba da wayoyi, mashina, da sauran abubuwan amfani.

Gwamnan jahar, Aminu Masari ya kai ziyara garin domin yi wa iyalan da abun ya shafa jaje.

Jihar ta Katsina dai na fuskantar matsalar rashin tsaro da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan, lamarin da har a kwanan baya ma ya sa gwamnan kokawa akai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Online view pixel