Dole-uwar-naki: Atiku ma da kan shi ya yadda Buhari zai kada shi zaben ranar Asabar

Dole-uwar-naki: Atiku ma da kan shi ya yadda Buhari zai kada shi zaben ranar Asabar

Shugaban jam'iyya mai mulki a Najeriya ta All Progressives Congress, (APC) watau Kwamrade Adams Oshiomhole yace dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, Alhaji Atiku Abubakar tuni ya amince ya fadi zaben da za'a gudanar a ranar Asabar.

Adams Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani akan kalaman da 'yan jam'iyyar ta PDP suka yi a taro na musamman da suka kira na 'yan kwamitin zartarwar jam'iyyar da yammacin ranar Talata akan maganar dage zabe.

Dole-uwar-naki: Atiku ma da kan shi ya yadda Buhari zai kada shi zaben ranar Asabar

Dole-uwar-naki: Atiku ma da kan shi ya yadda Buhari zai kada shi zaben ranar Asabar
Source: Facebook

KU KARANTA: Sheikh Gero yayi nadamar kalaman sa kan makiyan Buhari

Legit.ng Hausa ta samu cewa shugaban na APC ya bayyana cewa kalaman na Atiku inda yace wai jam'iyyar APC ta shirya yi masa magudi a shiyya biyu da yafi karfi a Najeriya a zaben da za'a gudanar ya tabbatar da cewa baya da magoya baya a sauran shiyyoyin na Najeriya hudu.

Ya kara da ceewa dukkan dan takarar da yake da magoya baya a sassan kasar nan biyu kadai a cikin shidda ba zai iya lashe zabe ba.

A wani labarin kuma, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya maka shugaba Buhari kotu kan aabun da ya kira rainin hankali.

Fitaccen dan siyasar, Atiku Abubakar dai ya shigar da karar ne yana kalubalantar shugaba Buhari da wata kungiyar dake goyon bayan sa kan rena masa hankali wajen kai shi kara a wata kotu ta daban inda ya bukaci ban hakuri daga gare su da kuma diyyar Naira biliyan 2.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel