Ra’ayin Shugaban INEC ya banbanta da na Buhari kan hukunta masu satar akwatin zabe

Ra’ayin Shugaban INEC ya banbanta da na Buhari kan hukunta masu satar akwatin zabe

Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zamanta (INEC), ya mayar da martani akan rudani da aka samu game da jawabi da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, inda yake cewa “a bakin ran” duk wanda yayi yunkurin sace akwatin zabe mai zuwa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranan Litinin, 18 ga watan fabrairu yace a kashe duk wanda yayi yunkurin sace akwatin zabe.

Haka zalika, yayinda shugaban hukumar zabe farfesa Yakubu yake mayar da martani akan jawabin shugaban kasar a ranan Talata, 19 ga watan Fabrairu, ya bayyana cewa ya kamata a hukunta masu sace akwatinan zabe kamar yanda doka ya tanadar.

Ra’ayin Shugaban INEC ya banbanta da na Buhari kan hukunta masu satar akwatin zabe

Ra’ayin Shugaban INEC ya banbanta da na Buhari kan hukunta masu satar akwatin zabe
Source: Original

A cewar Sahara Reporters, an gabatar da jawabin shugaban kasar ga shugaban hukumar INEC ne a lokacinda yake mika jawabai ga manema labarai akan shirye-shiryen hukuman don gudanar da zabbuka.

KU KARANTA KUMA: Allah ya riga ya zabi Atiku a matsayin Shugaban kasa na gaba – Prophet Udoka

Har ila yau, Yakubu ya musanta rahotanni dake cewa hukumar DSS ta gayyaci Okechukwu Ibeanu, babban kwamishinan hukumar INEC mai kulawa da sarrafa kayan aikin hukumar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa ayau, Talata, ne fadar shugaban kasa ta bayyana cewar jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga halin damuwa bayan shugaban kasa Muhammdu Buhari ya umarci jami’an tsaro da kar su tausaya wa duk wanda ya yi yunkurin gudu wa da akwatin kuri’u a zabukan da za a gudanar cikin watan Fabarairu da Maris.

Fadar shugaban kasa ta ce kalaman shugaba Buhari gargadi ne ga ‘yan siyasar da su ka mayar da satar akwatun kuri’u ta hanyar amfani da ‘yan daba al’ada a lokutan zabe.

Da ya ke Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, babban mai taimaka wa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Garba Shehu, ya ba boyayyen abu ba ne cewar wasu ‘yan siyasa na amfani da ‘yan ta’adda domin su sace akwatin kuri’u sannan su kashe ma su kada kuri’a ko kuma su raunata su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel