Ta kan N20,000 kudin beli, wani matashi ya mutu a hannun yan sanda

Ta kan N20,000 kudin beli, wani matashi ya mutu a hannun yan sanda

Wani mutumi mai suna Osifo Okeguare, ya mutu a hannun jami'an hukumar yan sanda a ofishin hukumar dake Ekpoma, karamar hukumar Esan a jihar Edo.

Legit.ng ta samu labarin cewa jami'an yan sandan sun tsare Osifo Okeguare ne bayan iyalansa sun gaza biyan kudin beli N20,000 da ofishin yan sandan ta bukata.

Wani dan fafutukan kare hakkin dan adam, Kola Edokpayi, ya bayyana cewa iyalan sun samu tara N15,000 amma babban jami'in dan sandan ya lashi takobin sai sun cika N5,000.

Amma, kakakin hukumar yan sandan jihar Edo, DSP Chidi Nwabuzor, ya ce Osifo da wani Richard Femi sun shiga hannun hukuma ne ranan 10 ga watan Febrairu yayinda sukayi kokarin sace wata Babur a garin.

Da hukuma ta kamashi ba da dadewa ba ya fara rashin lafiya kuma aka kaishi asibitin Eremosele da ke Ekpoma domin jinya amma ya cika a wajen.

A yanzu haka, Nwabuzor ya ce an ajiya gawarsa a dakin ajiye gawawwakin asibitin Iruekpen domin gudanar da bincike da sababin kisansa.

KU KARANTA: Rundunar hukumar sojin sama sun damke yan bindiga 10 a jihar Kaduna

Ya yi kira ga iyalan mamacin suyi hakuri kuma su bi doka zuwa lokacin da za'a kammala bincike akan gawar.

Hakazalika a makon nan, wani jami'in kwastam ya bindige wani mutumi kawai don ya hanashi cin hancin N5000 a bainar jama'a. Bayan duniya ta ga faifan bidiyon abinda ya faru, hukumar Kwastam ta saki jawabin cewa mutumin yayi kokarin kwace bindigan jami'an ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel