Jihar Yobe ta yi babban rashi: Mataimakin kakakin majalisar jihar ya rasu

Jihar Yobe ta yi babban rashi: Mataimakin kakakin majalisar jihar ya rasu

Labarin da muke samu yanzu na nuni da cewa Dr. Ibrahim Kurmi, mataimakin kakakin majalisar dokoki na jihar Yobe ya rasu a daren ranar Litinin, a asibitin koyarwa na jihar Yobe da ke Damaturu.

Alhaji Muhammad Wakil, daraktan watsa labarai na majalisar dokokin jihar, wanda ya tabbatar da mutuwar mataimakin kakakin majalisar ya ce Dr. Ibrahim ya rasu yana da shekaru 48 a duniya.

"Mun samu labarin mutuwar mataimakin kakakin majalisar dokoki a daren jiya (Litinin) bayan doguwar jinya, inda aka yi jana'izarsa da misalin karfe 11 na safiyar yau a gidansa da ke Damaturu. Hakika mun kadu matuka," a cewarsa

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Shirin TraderMoni ya samu babbar matsala a Abeokuta

Jihar Yobe ta yi babban rashi: Mataimakin kakakin majalisar jihar ya rasu

Jihar Yobe ta yi babban rashi: Mataimakin kakakin majalisar jihar ya rasu
Source: UGC

Kurmi, wanda likita ne, na wakiltar mazabar Fika/Gadaka a majalisar dokoki ta jihar, kuma a fara zabarsa a karon farko a matsayin mataimakin kakakin majalisar a 2011, kafin ya yi murabus a 2012.

An sake zabarsa domin wakiltar mazabarsa a 2015 inda a nan ma ya zama mataimakin kakakin majlisar, mukamin da ya ke rike da shi har zuwa lokacin mutuwarsa.

An haifi marigayin ne a ranar 23 ga watan Maris 1971, ya fara karatunsa a makarantar Firamare ta Kurmi a Yobe daga 1978 da 1984, ya halarci makarantar sakandire ta Biu a Borno daga 1985 zuwa 1992 da kuma jami'ar Maiduguri daga 1992 zuwa 2000.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel