Maganar gaskiya: Buhari na son ganin ana zubar da jinin 'yan Nigeria - Secondus

Maganar gaskiya: Buhari na son ganin ana zubar da jinin 'yan Nigeria - Secondus

Legit.ng Hausa ta samu rahoto kan cewa shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da zama silar zubar da jinin 'yan Nigeria. Haka zalika Secondus ya yi ikirarin cewa Buhari na son ganin an zubar da jinin 'yan Nigeria ne domin cimma wata manufarsa ta siyasa

Secondus ya yi wannan zargin ne a ranar Talata a taron gaggawa na majalisar zartaswar jam'iyyar, a matsayin martani ga barazanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar Litinin na cewar "duk wani wanda ya ke ganin yana da karfin ikon tara 'yan bangar siyasa su saci akwati ko tayar da tarzoma a wajen zabe, to kuwa zai yi hakan a bakin ransa."

Bayan gabatar da jawabi na tsawon mintuna, Secondus ya ce: "Kafin na kammala jawabin nawa, bari na kara jaddada cewa 'yan Nigeria sun gaji da mulkin shugaban kasa Buhari. Maganar gaskiya ita ce, sama da shekaru ukku, ana ci gaba da kashe mutane, amma a yau shugaban kasar ne ke bayar da umurnin a kashe mutane.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Taron majalisar zartaswa na PDP ya soma gudana a Abuja

Maganar gaskiya: Buhari na son ganin ana zubar da jinin 'yan Nigeria - Secondus

Maganar gaskiya: Buhari na son ganin ana zubar da jinin 'yan Nigeria - Secondus
Source: Depositphotos

Me ya sa kake son ganin an zubar da jini? Me ya sa kake son jini da yawa ne? Ina so na tambaye ka, Buhari, Me ya sa kake son ganin jinin 'yan Nigeria yana zuba ne?

"Me ya sa kake son ganin ana kashe maza da mata a kasarka kawai saboda zabe? Saboda tilas ne ka zama shugaban kasa? Kai kanka dai ka sani, kai ba Allah ba ne, ina kara tunasar da kai, kai ba Allah ba ne.

"Dukkanin wasu matakai da ka ke dauka tsawon shekarun nan ukku, ba kana yi ba ne saboda ci gaban al'ummar Nigeria; a mulkinka ne aka san Yunwa, karuwar kashe-kashe, rashin aikin yi; kuma duk baka da damu da su ba. Hatta a cikin jam'iyyarka, ka raba kawunan su. Ka zama shugaba azzalumi mayaudari."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel