Dan Abacha ya ba Buhari tabbacin samun kuri’u miliyan 2

Dan Abacha ya ba Buhari tabbacin samun kuri’u miliyan 2

- Dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar Advance Peoples Democratic Alliance (APDA) a jihar Kano, Mohammed Abacha ya nuna goyon bayansa ga kudirin tazarcen Shugaba Buhari

- Mohammed yayi alkawarin kawo wa Shugaban kasar akalla kuri’u miliyan biyu a jihar

- Yace yana goyon bayan Buhari saboda tarin nasarorin da ya samu tun bayan hawarsa karagar mulki

Mohammed Abacha, dan takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar Advance Peoples Democratic Alliance (APDA) a jihar Kano ya nuna goyon bayansa ga kudirin tazarcen Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mohammed yayi alkawarin kawo wa Shugaban kasar akalla kuri’u miliyan biyu a jihar.

Dan Abacha ya ba Buhari tabbacin samun kuri’u miliyan 2

Dan Abacha ya ba Buhari tabbacin samun kuri’u miliyan 2
Source: Getty Images

Baban dan marigayi tsohon shugaan kasar, Janar Sani Abacha ya kaddamar da goyon bayan dan takarar Shugaban kasar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a bainar jama’a, yayinda yake jawabi ga manema labarai a ofishin kamfen dinsa da ke hanyar Maguwa a Kano a ranar Litinin, 18 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Atiku zai kayar da Buhari da tazara mafi girma – Kungiyar kamfen tayi ikirari

Da farko dai dama jam’iyyar APDA na kasa ta kaddanar da goyon bayanta ga tazarcen Shugaban kasa.

Abacha, wanda ya samu wakilcin Bashir Bataya, Shugaban APDA a Kano, ya nuna goyon bayansa ga Buhari saboda tarin nasarorin da ya samu tun bayan hawarsa karagar mulki.

A cewarsa wasu daga cikin nasarorin Buhari sun hada da tsaro, daidaita tattalin arziki, manyan ayyuka da kuma habbaka harkar noma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel