Dage zabe: Rarara da Adam Zango sun saki sabbin wakokin Buhari da Atiku (Ku kalla)

Dage zabe: Rarara da Adam Zango sun saki sabbin wakokin Buhari da Atiku (Ku kalla)

Tun bayan daga zaben gama gari da hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a Najeriya tayi a daren ranar Juma'a wajen karfe 2 na dare, salon siyasar kasar ya canza kuma mutane suke cigaba da bayyana ra'ayoyin su kan hakan.

Sai dai kuma ana cikin hakan, kusan dukkan masu ruwa da tsaki a harkar suka cigaba da bayyana mabanbantan ra'ayoyin su akan hakan inda aka samu kusan dukkan bangarorin na jam'iyya mai mulki APC da kuma ta adawa ta PDP suna sukar hukumar ta INEC.

Dage zabe: Rarara da Adam Zango sun saki sabbin wakokin Buhari da Atiku (Ku kalla)

Dage zabe: Rarara da Adam Zango sun saki sabbin wakokin Buhari da Atiku (Ku kalla)
Source: UGC

KU KARANTA: Hotunan jiragen kasan da Buhari ya siyo

To tun da dai karin wa'adin zaben ya tabbata, fitattatun mawakan nan na masana'antar nishadi ta Hausa a bangaren siyasa tuni suka dukufa wajen baza basirar su don ganin sun zaburar da magoya bayan su don tabbatar da sun fito sun yi zabe.

Kamar dai a shekarar 2015 da hukumar ta INEC ta dake zaben da sati 6, inda kuma mawakin nan na jam'iyyar APC Dauda Kahutu Rarara ya yi wata wakar da ta shahara a bakunan mutane akan zaben da kuma Buhari, yanzu ma ya sake yin wata wakar.

Shima dai Adam A. Zango da ya bar tafiyar siyasar APC ya sauya sheka ya zuwa PDP da kuma tafiyar dan takarar ta Atiku Abubakar mun samu labarin cewa yayi tashi sabuwar wakar.

Ga dai wakokin na:

Ga ta Adam Zango nan:

Ga ta Rarara nan akan Buhari:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel