Karin tarago-taragon jiragen kasan da Buhari ya sawo sun iso Najeriya (Hotuna)

Karin tarago-taragon jiragen kasan da Buhari ya sawo sun iso Najeriya (Hotuna)

Sababin tarago-taragon jiragen kasan da gwamnatin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ta bayar da umurnin a siyo domin inganta harkokin sufuri a kasar sun soma isowa daga kasar Sin inda aka siyo su.

Hotunan jiragen kasan dai sun soma yawo ne a kafafen sadarwar zamani a dai dai inda wani jirgin ruwan da yayi dakon su yake sauke su ana kuma dora su a saman wasu manyan motocin sufuri da zummar kai su inda za'a hada su.

Karin tarago-taragon jiragen kasan da Buhari ya sawo sun iso Najeriya (Hotuna)

Karin tarago-taragon jiragen kasan da Buhari ya sawo sun iso Najeriya (Hotuna)
Source: Facebook

KU KARANTA: An kama mutum 2 da bindigogi a Zamfara

A baya dai mun taba kawo maku labarin jirgin kasa dake jigilar jama'ar da yayi sanadiyyar mutuwar wani saurayi mai shekaru 27 a duniya mai suna Paul a garin Abuja bayan da ya rumurmutse shi, jiya Juma'a da safe.

Da mahaifin matashin na karin bayani ga manema labarai, Mista Francis Idoko ya bayyana cewa lamarin yayi matukar kada masa hanta domin kuwa mutuwar ta girgiza shi matuka.

Legit.ng ta samu cewa mahaifin mamacin ya kara da cewa sun yi bankwana da dan na sa da safiyar juma'ar kafin ya fita zuwa wajen aiki har ma ya karbi Naira 200 a hannun sa da zai hau tasi.

Ga dai hotunan jiragen kasan nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel