Fada-da-aljani: Sojin Najeriya sun yi arangama da 'yan Boko Haram a Borno

Fada-da-aljani: Sojin Najeriya sun yi arangama da 'yan Boko Haram a Borno

Dakarun rundunar sojojin Najeriya na musamman dake a balaiya ta 231 da kuma 331 acan garin Biu sun sanar da samun nasarar yin raga-raga wasu 'yan ta'addan Boko Haram bayan sun yi masu kwantan bauna ranar Asabar 16 ga watan Fabreru.

Kamar dai yadda muka samu daga sanarwar da jami'ain hulda da jama'a na rundunar sojin Najeriya Kanal Sagir Musa ya bayyana, artabun nasu bai yiwa 'yan Boko Haram din ba domin kuwa sun ranta a na kare sannan kuma sun kwace makamai da dama daga hannun su.

Fada-da-aljani: Sojin Najeriya sun yi arangama da 'yan Boko Haram a Borno
Fada-da-aljani: Sojin Najeriya sun yi arangama da 'yan Boko Haram a Borno
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An kama mutum biyu da makamai a garin Gusau

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa cikin makaman da suka kwata a hannun 'yan ta'addan sun hada da bindigu 2 kirar AK 47, dozin dozin din harsasai, wasu layu na tsafi da kuma babur din hawan su.

A wani labarin kuma, akalla mutane 66 ne aka kashe a wasu unguwani da ke kusa da kauyen Maro Gida da ke karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna a wani hari da aka kai a daren jiya.

Cikin wadanda aka kashe akwai yara 22 da kuma mata 12 yayin jami'an tsaro sun ceto rayyukan wasu mutane hudu da suka jikkata kuma suna nan suka karbar magani a asibiti.

Rugagen da aka kai harin sun hada da Ruga Bahago, Ruga Daku, Ruga Ori, Ruga Haruna, Ruga Yukka Abubakar, Ruga Duni Kadiri, Ruga Shewuka and Ruga Shuaibu Yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel