Zamantakewar aure: Ali Nuhu ya bada labarin yadda ya hadu da matarsa har ya aureta

Zamantakewar aure: Ali Nuhu ya bada labarin yadda ya hadu da matarsa har ya aureta

Kamar yadda ya fara a matsayin jarumi, daga bisani ya koma mai daukar nauyin fina-finai har dai zuwa mai bayar da umurni, jarumi Ali Nuhu ya kasance kamar wani basarake a farfajiyar masana'antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. Ganin yadda kasuwa fina-finan hausa ke ja baya, hakan ya sa jarumin ya koma daukar fina-finan kudu da aka fi sani da Nollywood, ko a can, tauraruwarsa ta haska, inda ya zama sarki a gida kuma sarki a dawa.

Sai dai wani boyayyen sirri da kowa ya kasa ganewa shine yadda rayuwar zamantakewar auren jarumin take, da yawa na jinjina masa, ganin cewa ko sau daya ba a taba jin matarsa ta yi yaji ko an ji kansu ba, sabanin yadda aka saba ji a tsakanin sauran jaruman fim da suka yi aure, wasu har ta kaisu ga saki.

A zantawarsa da jaridar Daily Trust, jarumi Ali Nuhu ya labarta yadda ya hadu da matarsa, Maimuna, a wajen shirin daukar shaharren fim din nan 'Wasila'. Kamar yadda yake cewa: "Ina bakin aiki a lokacin, a shekarar 2000, na ga ta shiga cikin gidan da muke daukar fim a lokaci, cikin raha na ke sanar da abokan aikina, su Ishaq Sidi Ishaq da Hajara Usman, cewar na ga matar da zan aura. Kamar dai wasa, karamar magana ta zama babba, muka fahimci juna bayan da na tuntube ta. Bayan kwana biyu na bukaci mai daukar shirin fim din, Yakubu Lere, wanda dan uwanta ne, da cewar ina so na sake ganinta, da wannan muka fara sabawa da fahimtar junanmu."

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Rikici ya rutsa da hadimin gwamnan jihar Delta, an harbe shi har lahira

Zamantakewar aure: Ali Nuhu ya bada labarin yadda ya hadu da matarsa har ya aureta
Zamantakewar aure: Ali Nuhu ya bada labarin yadda ya hadu da matarsa har ya aureta
Asali: UGC

Ko da aka tambayi Ali Nuhu yadda yake kula da iyalansa da kuma aikinsa a lokaci daya, ganin yadda wahala da kuma daukar lokacin irin wannan aikin nasa, sai cewa ya yi: "Duk abunda zaka yi, kasance mai saka shi a sikeli domin auna shi da matsayin iyalinka. Kar ka bari aikinka ya rinjayi martabar iyalinka." Ya kuma ce dole ne mutum ya kasance mai wadatar da iyalansa da duk abubuwan da suke bukata, yana mai cewa, "muna kasancewa tare da juna, komai dadi komai rashinsa."

Haka zalika Ali Nuhu ya zayyana wasu muhimman matakai da ya kamata kowa ya rike idan har yana son dorewar zamantakewarsa da iyalansa da suka hada: "Ka kasance mai kaifi daya. Ka kasance mai nuna soyayyarka ga matarka da 'yayanka. Ka kasance mai baiwa 'yayanka damar daukarka a matsayin babban abokinka, kuma karka ce lallai sai sun bi ra'ayinka idan ya zo wajen zabar fannin da za su yi karatu ko aiki a rayuwarsu," a cewar sa.

Yawaitar saki a Arewacin Nigeria, a cewar Nuhu, yana faruwa ne saboda da yawan mazaje ba su mayar da hankali wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu. "Kuma da yawa na kallon mata a matsayin ababen kore sha'awa. Nuna kauna, jin kai da kulawa, wadanda ko a Musulunci na daga cikin shika shikan aure, an yi watsi da su."

Ali Nuhu ya bayyana cewa matarsa ta kasance mai bashi kwarin guiwa a dukkanin lamuransa, tun kafin ma ya aureta. "Ta fahimci aikina, kuma ta taimaka mun kwarai wajen cire duk wani kokonto akan yadda nake a majigi da kuma yadda nake a fili. Ita da kanta ta dauki nauyin fina-finai na guda ukku, ciki har da "Madubin Dubawa', 'Son Mai So' da kuma 'Janjani"

"Duk da irin rashin lokacina, na rashin zama gida. Amma na kan ware lokuta domin kasance tare da iyalina da kuma sauke nauyin da ya rataya a wuyana na miji da kuma uba," a cewar Nuhu, yana mai cewa: "Wasu lokutan na kan dauke su muje shakatawa ta iyali wasu garuruwa, mu samu lokacin kasancewa tare da junanmu, kawai saboda rama masu lokutan da bana tare da su."

A bangaren kasancewar uba, Nuhu ya ce: "Ina jin dadin yadda nake daukar yarana na kaisu makaranta kuma na dauko su idan sun tashi. Ina jin dadin kyakkyawar alakar da ke a tsakaninmu. Hakika yara ne na-gari."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel