Kwankwaso ya yi godiya ga mutanen Kano kan yadda suka yi tururuwar fitowa kamfen din PDP

Kwankwaso ya yi godiya ga mutanen Kano kan yadda suka yi tururuwar fitowa kamfen din PDP

- Sanata Rabi’u Kwankwaso ya yaba ma mutanen Kano kan tururuwar fitowa da suka yi a gangamin kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP da ya gudana a filin wasa na Sani Abacha a ranar 10 ga watan Fabrairu

- Kwankwaso ya mika godiyan ne yayinda yake jawabi ga malaman addinin Musulunci da suka kai masa ziyarar ban girma gidansa da ke Kano

- Tsohon gwamnan na jihar Kano, ya bayyana cewa dandazon da suka hallara a wajen gangamin ya nuna karara cewa mutanen Kano na PDP ne

Sanata mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Alhaji Rabi’u Kwankwaso ya yaba ma mutanen Kano kan tururuwar fitowa da suka yi a gangamin kamfen din dan takarar shugaban kasa na PDP da ya gudana a filin wasa na Sani Abacha a ranar 10 ga watan Fabrairu.

Kwankwaso ya mika godiyan ne yayinda yake jawabi ga malaman addinin Musulunci da suka kai masa ziyarar ban girma gidansa da ke Kano a daren ranar Alhamis, 14 ga watan Fabrairu.

Kwankwaso ya yi godiya ga mutanen Kano kan yadda suka yi tururuwar fitowa kamfen din PDP
Kwankwaso ya yi godiya ga mutanen Kano kan yadda suka yi tururuwar fitowa kamfen din PDP
Source: Twitter

Kwankwaso wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Kano, ya bayyana cewa dandazon da suka hallara a wajen gangamin ya nuna karara cewa mutanen Kano na PDP.

Ya shawarci malaman Musulunci a jihar da su guji tsoma baki cikin siyasa maimakon haka suyi amfani da matsayinsu na malaman addini su shawarci mutanensu kan yadda za su samu shugabanci nagari.

KU KARANTA KUMA: Saraki yayi kuskuren nema wa shugaba Buhari kuri’u 90% a Kwara (bidiyo)

Ya yi kira ga mutanen Kano da su zabi yan takarar PDP a dukkan matakai, inda ya kara fa cewa masu zabe suyi amfani da zuciyarsu wajen zabar yan takara da shugabanni nagari, tare da hangen nesa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel