Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Ga gwamnonin Najeriya da suka kare wa'adinsu na shekaru 8, komawa majalisar dokokin tarayya ya zama ruwan dare. Tunda kundin tsarin mulkin Najeriya bata amince da tazarce ba, yan siyasa tun gano cewa kareshe rayuwarsu a majalisar dattawa shine kare mutuncinsu.

Yanzu haka majalisar dattawa ta zama gidan ritayan gwamnoni kuma bayan zaben ranan Asabar, da yiwuwan yawansu ya karu.

A yau, tsaffin gwamnonin da ke majalisar dattawa sune Jonah Jang (Plateau), Bukola Saraki (Kwara), Joshua Dariye (Plateau), Rabiu Kwankwaso (Kano), Aliyu Wamakko (Sokoto), Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Bukar Abba Ibrahim (Yobe), George Akume (Benue) and Theodore Orji (Abia).

Legit.ng hausa ta kawo muku jerin gwamnoni dake takaran kujerar sanata a zaben da za'a gudanar gobe:

1. Ajibola Ajimobi

Ajimobi ya zama gwamnan jihar Oyo a shekarar 2011 karkashin jam'iyyar Action Congress kafin hadin gambiza da APC. Ya lashe takararsa karo na biyu a jam'iyyar APC inda ya karya tarihi a jihar Oyo.

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe
Source: Depositphotos

2. Rochas Okorocha

Okorocha ya kasance a faggen siyasan Najeriya tun shekarar 1999 inda ya fadi a zaben gwamna. Daga baya yayi takaran kujeran shugaban kasa ya sake fadi. A shekarar 2011 ya lashe zaben gwamnan jihar Imo karkashin jam'iyyar APGA.

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe
Source: UGC

3. Ibikunle Amosun

Amosun, wanda ya kasance Sanata tsakanin shekarar 2003 da 2007 ya zama gwamna a shekarar 2100 kuma ya sake lashewa a 2015. A yanzu haka, ya rantse sai ya koma majalisar dattawa domin wakiltan jama'a mazabar Ogun ta tsakiya.

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe
Source: Twitter

4. Ibrahim Dankwambo

Dankwambo ya kasance shahrarren akawu kafin shiga siyasa. Ya yi aiki a bankin CBN tsakanin shekarar 1988 da 1999 inda aka nadashi akawun jihar Gombe.

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe
Source: Depositphotos

Daga baya ya zama akawun gwamnatin tarayya a shekarar 2005. Daga nan yayi takaran gwamnan jihar Gombe kuma ya lashe.

5. AbdulAziz Yari

Gwamnan jihar Zamfara wanda ke cikin shekararsa ta takwas ya hana uban gidansa, Ahmed Sani Yarima, takarar kujerar wannan karon saboda yana son maye gurbinsa. Ya kasance dan majalisan wakilai a shekarar 2007 karkashin jam'iyyar ANPP.

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe
Source: Facebook

6.Ibrahim Gaidam

Yayinda wa'adinsa zata kare a watan Mayun 2019, Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam, ya shirya tsaf domin komawa majalisar dattawa inda ya lashe zaben ranan Asabar.

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe
Source: UGC

7. Kashim Ibrahim Shettima

Gwamnan jihar Borno, Kashim Ibrahim Shettima, ya shiga takaran kujeran sanata mai wakilta Borno ta tsakiya inda yake shirin maye gurbin Baba Kaka Garbai.

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe
Source: Depositphotos

8. Tanko Almakura

Gwamnan jihar Nasarawa, Umar Tanko Almakura, na shirin kwace kujerar sanata Suleiman Adokwe na jam'iyyar PDP wanda yake majalisar tun shekarar 2007.

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe

Gwamnoni 8 masu takaran kujeran Sanata gobe
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel