Kotu ta sake gurfanar da dan takaran gwamna na PDP a Niger da tsohon gwamna kan zambar N4.56b

Kotu ta sake gurfanar da dan takaran gwamna na PDP a Niger da tsohon gwamna kan zambar N4.56b

Dan takaran kujeran gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Niger, Umar Nasko da kuma tsohon gwamnan jihar, Babangida Aliyu a ranar Alhamis sun gurfana a gaban babbar kotun dake Minna bisa zargin zamba.

Wadanda ake zargin biyu na fuskantar tuhuma tare da shugaban jam’iyyar PDP, Tanko Beji bisa zargin zambar kudi kimanin naira biliyan 4.568 da aka karkatar na aikin kiyaye lafiyar muhalli.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa Justis Aliyu Mayaki ne ya fara sauraran karan inda ya daga sauraran karan har zuwa 4 ga watan Maris.

Kotu ta sake gurfanar da dan takaran gwamna na PDP a Niger da tsohon gwamna kan zambar N4.56b
Kotu ta sake gurfanar da dan takaran gwamna na PDP a Niger da tsohon gwamna kan zambar N4.56b
Asali: UGC

Duk da haka, ya sake nada Justis Mohammed Mohammed dake babban kotun jihar don sake sauraran karan daga farko a ranar Alhamis.

A lokacin da aka karantowa wadanda ake zargin laifuffukansu, duk basu amsa laifi ba.

KU KARANTA KUMA: Zan shafe ta’addanci daga kasar nan idan har aka zabe ni a karo na biyu - Buhari

Mohammed ya bukaci wadanda ake zargin da su cigaba da cin morriyar belin da justis Aliyi Mayaki ya basu a baya sannan zasu mikawa kotun takardunsu na tafiya kasashen ketare. Saboda haka, ya daga shari'an har zuwa 21 da 22 ga watan Fabrairu don ci gaba da sauraron karan.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa a ranar Laraba jam’iyyar PDP ta gabatar da jawabi ta hannun darektan sadarwa na kungiyar Nasko Campaign Organisation, Yahaya Usman, inda yayi zargin cewa sauya masu shari’a da aka yi ya kasance shiri ne don karkatar da hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel