Duk zance ne, nine kadai na ke da masaniyar waye zai lashe zaben shugaban kasa - Guru Maharaj

Duk zance ne, nine kadai na ke da masaniyar waye zai lashe zaben shugaban kasa - Guru Maharaj

- Guru Maharaj Ji, ya yaba ma yaki da rashawar shugaba Muhammadu Buhari

- Maharaj Ji, ya bayyana cewa yana da ikon da zai sa Buhari zama shugaban kasa a zaben ranar Asabar mai zuwa

Fitaccen matsafin nan mai suna , Sat Guru Maharaj Ji, ya bayyana cewa yana da ikon da zai sa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zama shugaban kasa a zaben ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu mai zuwa.

A wata hira da jaridar Premium Times, shahararren matsafin ya ce koda dai dukkanin gwamnatocin baya sun yi kokari sosai, a nashi ra’ayin ya yaba da yaki da cin hanci da rasawar Shugaban kasa Buhari.

Duk zance ne, nine kadai na ke da masaniyar waye zai lashe zaben shugaban kasa - Guru Maharaj
Duk zance ne, nine kadai na ke da masaniyar waye zai lashe zaben shugaban kasa - Guru Maharaj
Asali: Original

Maharaji Ji, ya kuma bayyana cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen fada ma Buhari gaskiya kamar yadda yake yawan shawartar tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a kai- akai a baya.

Ya kuma bayyana cewa duk zance masu hasashen wanda zai lashe zae ke yi cewa shi kadai ne ya san wanda zai zama shugaban kasa a zaben karshen makon nan.

KU KARANTA KUMA: Nasara ko fadu wa: Buhari ya roki Atiku ya karbi sakamakon zabe

Duk zance ne, nine kadai na ke da masaniyar waye zai lashe zaben shugaban kasa - Guru Maharaj
Duk zance ne, nine kadai na ke da masaniyar waye zai lashe zaben shugaban kasa - Guru Maharaj
Asali: UGC

Yace: “A gobe, a bari a gani idan Buhari ya yi martani mara kyau zan fada masa a jaridu kowa zai ji. Cewa a’a ba za iya kaiwa wajen ba, ina da ikon nada ka a matsayin Shugaban kasa.

“Duba, a shekarar bara nayi Magana game da nada wani dan Igbo ya zama Shugaban kasa. Ikedife (tsoon Shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo), mun yi wata ganawa, ban san mai suka tattauna ba, suka sanya shi rubuta wani suka a jaridu, bai san cewa na san tarko suka dana mai ba cikin watanni shida, yallabai ya canja jiki.”

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Maharaj Ji ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bola Tinubu da sauran masu fada aji a kasar da su hada kansu sannan su samar da mafita ga rikicin makiyyaya a Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

]

Asali: Legit.ng

Online view pixel