Cin mutunci: An kama wasu garada uku da su ka zuba barkono a gaban wata budurwa

Cin mutunci: An kama wasu garada uku da su ka zuba barkono a gaban wata budurwa

Wata babbar kotu da ke garin Benin, babban birnin jihar Edo, ta yi umarni a tsare wasu mutan uku a gidan yari bayan gurfanar da su bisa tuhumar su da laifin sace wata budurwa mai suna Favour Ada Friday tare da zuba ma ta dakakken barkono a ‘yan matancin ta.

Kartin uku da aka gurfanar sun hada da shugaban ‘yan bijilanti na unguwar Ugbiyoko, Mista Lucky Igbinovia, Joel Otoghile da Iyamu Kingsley.

An gurfanar da su a gaban kotun ne bisa tuhuma 14 da su ka hada da yumkurin aikata kisa, garkuwa da mutum, da kuma zuba sinadari mai cutar wa a farjin Favour.

Cin mutunci: An kama wasu garada uku da su ka zuba barkono a gaban wata budurwa
Cin mutunci: An kama wasu garada uku da su ka zuba barkono a gaban wata budurwa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa al'ummar Adamawa za su zabi Buhari - Talban Adamawa

Ragowar tuhumar sun hada da cin mutunci, kwace, da yada faifan bidiyon tsiraicin budurwar da su ka azabtar.

Lauya mai gabatar da kara, Peter Ugwumba, ne ya roki kotun da ta aika wadanda aka gurfanar gidan yari kafin darektan gurfanarwa da shari’a na jihar Edo ya bayar da shawara a kan tuhumar da ake wa mutanen.

Mutanen sun azabtar da Favour ne bayan sun kama ta bisa zargin cewar ta saci wayar hannu.

Sai dai, Ugwumba ya shaida wa kotu cewar bincike ya tabbatar da cewar babu wata waya da budurwar ta sata.

Bayan sauraron korafin lauya Ugwumba, alkalin kotun, Jastis Acha, ya bayar da umarnin tisa keyar mutanen uku zuwa gidan yari har zuwa ranar 6 ga watan Maris da za a cigaba da sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel