Rana bata karya: Yau APC za ta san matsayinta a Kotun Koli

Rana bata karya: Yau APC za ta san matsayinta a Kotun Koli

- Ana sanya ran jam'iyyar APC reshen jihar Rivers za ta san matsayinta a yau

- Kotun Koli za ta yanke hukunci dangane da saukaka kara da jam'iyyar tayi akan tsayar da dan takararta a jihar Rivers

- An dai samu rabuwar kai ne akan wanda zai tsaya takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar

Rahotanni sun kawo cewa a yau Talata, 12 ga watan Fabrairu ne Kotun koli a Najeriya za ta yanke hukunci kan daukaka karar da jam'iyyar APC mai mulki a kasar ta yi dangane da tsayar da dan takarar gwamnan jihar Rivers da ke kudancin Najeriya.

Bangarori biyu na takardama da juna a siyasar jihar, kuma wannan karar ta biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara ta Najeriya ne da ya tabbatar da wani hukuncin na babbar kotun jihar ta Rivers wanda ya soke zaben fidda gwani da wani bangare na jam'iyyar ya gudanar.

Bangare guda na mara wa ministan gwamnatin Muhammadu Buhari wato Rotimi Amaechi baya, yayinda bangare guda kuma ke goyon bayan Sanata Magnus Abe.

Rana bata karya: Yau APC za ta san matsayinta a Kotun Koli
Rana bata karya: Yau APC za ta san matsayinta a Kotun Koli
Asali: Twitter

Ana sa ran kotun kolin za ta yanke hukunci karkashin alkalin kotun Bode Rhodes-Vivour a ranar Talata.

A wani lamari na daban, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya yi fatali da yunkurin babbar jam'iyyar adawa ta PDP na sake dawowa shugabancin Nigeria, yana mai cewa PDP na son ta dawo mulki ne kawai domin lalata duk wani ci gaba da shugaban kasa Buhari ya kawowa kasar tare da jan koma baya ga dukkanin ayyukan da ya tsara domin amfanar masu zuwa kasar a karnoni na gaba.

KU KARANTA KUMA: Rikicin SDP ya dauki sabon salo yayinda bangaren Gana suka mara wa Atiku baya

Da ya ke karbar bakuncin mataimakin shugaban APC na kasa reshen shiyyar Arewa da kuma jagoran kungiyar goyon bayan tazarcen Buhari, Sanata Lawal Shuaibu, gidan gwamnatin Katsina a jiya Litinin, Masari ya yi ikirarin cewa baiwa PDP wata damar zai sake mayar da kasar a halin da ta tsinci kanta na tsawon shekaru 16 na mulkinta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel