Daga-karshe: 'Yan shi'a sun bayyana matsayar su game da zaben su tsakanin Buhari da Atiku

Daga-karshe: 'Yan shi'a sun bayyana matsayar su game da zaben su tsakanin Buhari da Atiku

Kungiyar nan dake ikirarin gwagwarmaya ta addinin Musulunci a Nijeriya, wadda aka fi sani da ‘yan shi’a bangaren Sheikh Ibrahim Zakzaky sun nisanta kansu daga wasu rahotannin dake yawo na cewa tana goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa.

Kungiyar dai ta bayyana haka ne a wata takardar manema labarai da ta fitar dauke da sa hannun Malam Shu’abu Isa Ahmad na dandalin dalibai (Academic Forum) inda ya bayyana cewa labarin kanzon kurege ne da aka yada don a bata sunan kungiyar a idon mabiyan ta.

Daga-karshe: 'Yan shi'a sun bayyana matsayar su game da zaben su tsakanin Buhari da Atiku
Daga-karshe: 'Yan shi'a sun bayyana matsayar su game da zaben su tsakanin Buhari da Atiku
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Dan Arewa ya kirkiri na'urar da ta girgiza duniyar fasaha

Legit ng Hausa ta samu haka zalika cewa Malam Shu’iabu ya kuma bayyana cewa kungiyar ko jagoran su Sheikh Zakzaky da yanzu haka yake a hannun jami'an tsaro basu taba shiga harkokin siyasa kai tsaye ba ko nuna goyon bayan su ga wani dan takara ba.

Amma kuma daga karshe sai sanarwar ta yi wani bayani mai kama da gugar zana inda ta yabawa dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a bisa yadda suka ce ya yi tir da zaluncin ca ake yi wa Shaikh Zakzaky da jama’arsa.

Haka zalika sai yayi kira ga gwamnatin ta shugaba Buhari da ta gaggauta sakin jagoran nasu Shaikh Zakzaky da matarsa Zeenah Ibraheem da Deji Adeyanju da kuma sauran ‘yan Nijeriya da suke garkame a fadin tarayyar kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel