Arewa-gida: Dan Arewa ya kirkiri na'urar da za ta sa mota ta tuka kanta

Arewa-gida: Dan Arewa ya kirkiri na'urar da za ta sa mota ta tuka kanta

Wani shehin malamin zamani daga yankin Arewacin Najeriya Dakta Idris Ahmed da yake da digirin digirgir a fannin ilimin 'Cryptology' dake zaman haifaffen garin Mubi jihar Adamawa mazaunin birnin Coventry a Kasar Burtaniya ya kafa tarihi.

Dakta Idris Ahmed dai ya girgiza duniyar fasaha ne bayan da ya samu nasarar kirkira tare kuma da assassa fasahar tsaro na na'ura mai kwakwalwa da za'a yi anfani da ita akan mota wacce za ta iya tuka kanta.

Arewa-gida: Dan Arewa ya kirkiri na'urar da za ta sa mota ta tuka kanta

Arewa-gida: Dan Arewa ya kirkiri na'urar da za ta sa mota ta tuka kanta
Source: Facebook

KU KARANTA: APC ta shiga sabon rudu a jihar Zamfara

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa sanannen kamfanin kera mota na duniya dake Kasar Burtaniya wato "Jaguar Land Rover" ne suka baiwa kamfanin Dakta Idris Ahmed kwangila tun kusan shekara daya da ya gabata domin yayi aikin gina musu fasahar tsaro na na'ura mai kwakwalwar.

Kamar yadda muka samu dai cewa ita fasahar tsaron da ya kirkira an yi ta ne ta yadda ba za'a iya yiwa motar kutse (hacking) ba, wacce zata iya tuka kanta taje ko'ina ta dawo ba tare da direba ba.

A wani labarin kuma, Wani matashi dake ikirarin zama dan a-mutun shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar tazarce a jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) watau Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Adamu Kabir Matazu yayi barazanar kashe kan sa idan Buharin ya fadi zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel