Yanzu-yanzu: An damke jigon PDP, Yaro Makama, da yayi kira ga a kisan jami'an zabe

Yanzu-yanzu: An damke jigon PDP, Yaro Makama, da yayi kira ga a kisan jami'an zabe

Hukumar yan sandan Najeriya ta damke babban jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kaduna,Alhaji Yaro Makama rigachikun. Wannan na faruwa ne bayan damke kakakin yakin neman zaben PDP a jihar, Bako Ben.

An damke Yaro Makama ne kan zargin kira ga kisan jami'an hukumar INEC idan suka sanar da sakamakon da PDP bata amince da shi ba.

Mataimakin Kakakin PDP a jihar, Danjuma Sarki, ya bayyana hakan ne inda yace: " Da safen nan, an gayyaci Yaro Makama ofishin hukumar yan sanda. Ya amsa gayyatar a matsayinsa na mai bin doka.

"Sun tuhumcesa da maganar batanci kuma sun bukacesa da ya rubuta jawabi. Mun yi tunanin cewa bayan rubuta jawabin za'a sakeshi amma abin mamaki, sai suka tafi da shi Abuja."

A baya mun kawo muku cewa Wata bidiyo ta bayyana a shafin ra'ayi da sada zumunta inda wani da siyasa ya ke magana da babban murya yana kira ga mabiyan jam'iyyarsa su hallaka duk alkalin zaben da ya sanar da sakamakon da basu yarda da shi ba.

Wannan abin takaici ya faru ne a jihar Kaduna inda jigo a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP ya ke magana a filin yakin neman zaben dan takaran gwamnan jihar, Isa Ashiru Kudan.

Alkaluma sun bayyana cewa wanda yake wannan magana tsohon shugaban jam'iyyar PDP ne mai suna, Alhaji Yaro Makama. Ya yi wannan jawabin ne a gaban dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Isah Ashiru da Sanata Suleiman Hunkuyi kuma.

Isa Ashiru Kudan wanda ya kasance dan majalisan wakilai a gwamnatin baya da Sanata Suleiman Hunkuyi har yanzu basu nisanta kansa daga wannan jawabi da jigon jam'iyyar yayi ba.

Yace: "Duk uban da ya tawo ba da sakamako da jama'a suka amince da shi ba, toh billahi lazi ana karban sakamako ana kaishi kabarinshi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel