Baya-ba zane: Diyar Buba Galadima ta halarci taron gangamin kamfe din Buhari na Legas

Baya-ba zane: Diyar Buba Galadima ta halarci taron gangamin kamfe din Buhari na Legas

A wani yanayi mai kama da maganar nan ta Hausawa da ake cewa 'in ka haifi mutum, baka haifi halin sa ba, an ga diyar fitaccen dan adawar nan na Shugaba Buhari a yanzu kuma tsohon aminin sa a siyasance, Injiniya Buba Galadima a taron gangamin kamfe din Buhari na jihar Legas.

Zuwan na Zainab Buba Galadima dai yayi ta jawo cece kuce tare da tayar da kura musamman ma a kafafen sadarwar zamani tun bayan bullar hoton ta tare da mai magana da yawun kwamitin kamfe din yakin neman zaben Shugaba Buhari, Festus Keyamo.

Baya-ba zane: Diyar Buba Galadima ta halarci taron gangamin kamfe din Buhari na Legas

Baya-ba zane: Diyar Buba Galadima ta halarci taron gangamin kamfe din Buhari na Legas
Source: Facebook

KU KARANTA: Haraji: Buhari zai soma neman attajirai 85,000

Legit.ng Hausa ta samu cewa mutane dai na maganar cewa kamar akwai darasi babba a cikin hakan musamman ma ganin yadda shi mahaifin nata ke zaman na gaba-gaba wajen adawa da shugaba Muhammadu Buhari daga bangaren Atiku Abubakar.

Ita dai diyar ta Injiniya Buba Galadima kamar yadda muka samu tana aiki ne a fadar shugaban kasar na Najeriya kuma tana goyon bayan sa duk kuwa da matsayar mahaifin ta a kan hakan.

A wani labarin kuma, Shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya, Sheikh Yakubu Musa Hassan ya karyata rahoton da ake ta yadawa wai majalisar ta zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar dan takaran ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel