Da duminsa: Uwar gidan gwamnan Kogi ta yi hatsari a inda jirgin Osinbajo ya fado

Da duminsa: Uwar gidan gwamnan Kogi ta yi hatsari a inda jirgin Osinbajo ya fado

Amina Bello, uwar gidan gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ta gamu da hatsarin mota a garin Kabba, yankin da jirgin da ke dauke da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya fado a makon da ya gabata.

Uwar gidan gwamnan jihar Kogi, Amina Bello tare da sauran tawagarta, sun tsira da rayukansu ba tare da jin munanan raunuka ba, bayan da hatsarin mota ya rutsa da su a Kabba.

Da ya ke tabbatar da faruwar hatsarin a ranar Lahadi, babban sakataren watsa labarai na gwamnan jihar, Onogwu Muhammed, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a kusa da garin Oshokoshoko, karamar hukumar Kabba, a kan hanyar uwar gidan gwamnan zuwa garin Isanlu domin kaddamar da yakin zaben matan jam'iyyar APC.

KARANTA WANNAN: Zaben 16 ga Fabreru: Kai ke da nasara - Oba na Legas ya yiwa Buhari albishir

Da duminsa: Uwar gidan gwamnan Kogi ta yi hatsari a inda jirgin Osinbajo ya fado

Da duminsa: Uwar gidan gwamnan Kogi ta yi hatsari a inda jirgin Osinbajo ya fado
Source: Twitter

Ya ce uwar gidan gwamnan tare da hadiman gwamnan guda uku sun tsira da rayukansu a cikin hatsarin da ya auku a safiyar ranar Asabar.

Ya ce gwamnatin jihar ta godewa Allah da ya kubutar da rayuwar uwar gidan gwamnan da tawagarta.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel