Subul-da-baka: Kawo karshen rashin tsaron jihar Zamfara ba yanzu ba - Gwamna Yari

Subul-da-baka: Kawo karshen rashin tsaron jihar Zamfara ba yanzu ba - Gwamna Yari

Gwamnan jihar Zamfara dake a yankin Arewa maso yammacin kasar nan da kuma ke zaman shugaban gwamnonin Najeriya, Alhaji Abdulaziz Yari ya ce hakikanin gaskiya kawo karshen rashin tsaron da ake fama da shi a jihar tasa ba yanzu ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi sadda ya kai wa Sarkin masarautar Maradun a karamar hukumar Maradun din dake a jihar ziyarar ban-girma a fadar sa a cigaba da gangamin yakin neman zaben da yake yi a jihar.

Subul-da-baka: Kawo karshen rashin tsaron jihar Zamfara ba yanzu ba - Gwamna Yari

Subul-da-baka: Kawo karshen rashin tsaron jihar Zamfara ba yanzu ba - Gwamna Yari
Source: Twitter

KU KARANTA: Magidanci ya arce bayan matar sa ta haifi 'yan uku

Legit.ng Hausa ta tsinkayi majiyar mu ta kamfanin dillacin Labarai ta NAN tana cewa gwamnan yace saboda yadda kashe-kashen da satar mutanen da ake yi a jihar ya koma tamkar wata masana'anta da kasuwanci, sai an kai ruwa rana kafin a samu tsaro.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jihar ta Zamfara dai na fama da matsaloli na rashin tsaro kama daga fashi da makami da ma satar mutane domin garkuwa kusan shekaru 6 da suka gabata.

A wani labarin kuma, Kasar Amurka ta bayyana cewa sakamakon zaben gama gari da za'a gudanar nan ba da dadewa a tarayyar Najeriya yana da matukar muhimmaci a gareta da ma dukkan daukacin kashen duniya baki daya.

Jakadan kasar ta Amurka a kasar Najeriya Mista Stuart Symington shi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ya kammala wata ganawar sirri da gwamnan jihar Nasarawa, Gwamna Tanko Al-makura a ofishin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel