Baki-ke-yanka-wuya: Wani jigon PDP a Kaduna ya furta kalaman da suka jefa shi a tsomomuwa

Baki-ke-yanka-wuya: Wani jigon PDP a Kaduna ya furta kalaman da suka jefa shi a tsomomuwa

Wani jigo a jam’iyyar PDP na jihar Kaduna da shine darektan yada labaran jam’iyyar, ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar a jihar Kaduna da su lakadawa duk wanda ya zabi wata jam’iyya da ba jam’iyyar PDP ba dukan tsiya sannan su tabbata sun kwana da shirin ko ta kwana a jihar.

Ben Bako ya bayyana haka ne a taron kamfen din jam’iyyar a garin Kafanchan.

Baki-ke-yanka-wuya: Wani jigon PDP a Kaduna ya furta kalaman da suka jefa shi a tsomomuwa

Baki-ke-yanka-wuya: Wani jigon PDP a Kaduna ya furta kalaman da suka jefa shi a tsomomuwa
Source: UGC

KU KARANTA: Wani dan Arewa ya kera jirgin sama

Legit.ng Hausa da ta ga bidiyon Bako ya kara da cewa duk wanda ya tare su a hanya a lokacin da suke dakon kuri’u daga kauyukan su su tabbata sun yi masa dukan tsiya sannan su yi ta haka har sai sun iso garin Kafanchan inda za a tattara kuri’u.

Idan ba a manta ba a irin haka ne gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai shima ya zaro wasu kalamai inda yake cewa duk wanda ya saka wa Najeriya baki a harkokin zaben ta za a koma gida da gawar sa. Wannan magana ya tada wa mutane da dama hankali da har sai da gwamna El-Rufai ya fito ya wanke kansa, Cewa ba abinda yake nufi ba kenan.

Sai dai kuma shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa lallai zai tabbata ba a tada yamutsi a lokacin zabe ba, yana mai cewa burin sa shine ayi zabe lafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel