Sanayya-mai-rana: Ku sadu da Atiku Abubakar, iyalan sa da kuma 'ya'yan sa

Sanayya-mai-rana: Ku sadu da Atiku Abubakar, iyalan sa da kuma 'ya'yan sa

Tun bayan rahoton da muka kawo maku na iyalan Shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugabancin kasar a karo na biyu a jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari muke ta samun sakonni daga al'umma na bukar shi ma na dan takarar shugabancin kasar a PDP, Atiku Abubakar.

Dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyan PDP, Atiku yanzu haka yana da mata 4 da 'ya'ya 28.

An haifi Atiku Abubakar ranar 25 ga Nuwambar 1946 a kauyen Jada a jihar Adamawa.

Sanayya-mai-rana: Ku sadu da Atiku Abubakar, iyalan sa da kuma 'ya'yan sa
Sanayya-mai-rana: Ku sadu da Atiku Abubakar, iyalan sa da kuma 'ya'yan sa
Asali: UGC

KU KARANTA: Rayuwa, 'ya'ya da kuma labarin iyalan shugaba Buhari

Aure-auren sa:

Atiku ya auri matarsa ta fari Titilayo Albert a Disambar 1971 a Legas, a lokacin tana da shekara 19.

A watan Janairun 1979, Atiku ya auri matarsa ta biyu Ladi Yakubu.

A shekarar 1983 ya auri matarsa ta uku, Gimbiya Rukayya wacce 'ya ce ga marigayi Lamidon Adamawa, Aliyu Musdafa.

Ya auri matarsa ta hudu Fatima Shettima a shekarar 1986.

Daga baya auren Atiku Abubakar da Ladi ya zo karshe, sai ya auri Jennifer Douglas (Jamila).

'Ya'yan sa:

Titi 'yar asalin garin Ilesa ce, a jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta haifi 'yarta ta fari tare da Atiku Abubakar, Fatima. Daga nan sai ta haifi Adamu da Halima da kuma Aminu.

Sun haifi yara shida da Ladi. Su ne Abba da Atiku da Zainab da Hauwa (Ummi) da Maryam da kuma Rukaiya.

Gimbiya Rukayya wacce 'ya ce ga marigayi Lamidon Adamawa, Aliyu Musdafa ta haifi Aisha da Hadiza da Aliyu da Asma'u da Mustafa da Laila da kuma Abdulsalam.

Fatima Shettima ta haifi 'yarta ta fari Amina, sai ta haifi Mohammed sai ta yi tagwaye sau biyu Ahmed da Shehu da kuma Zainab da Aisha sannan 'yar auta Hafsat.

Jennifer (Jamila) ta haifi 'ya'ya uku da Atiku Abubakar, wato Faisal da Zahra da kuma Abdulmalik.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel