Gwamnati ta koka da yadda Iyaye ke yi wa 'Ya 'yan su ciki a Jihar Edo kamar hauka

Gwamnati ta koka da yadda Iyaye ke yi wa 'Ya 'yan su ciki a Jihar Edo kamar hauka

- Gwamnati ta koka da yadda Iyaye ke yi wa 'Ya 'yan su ciki a Jihar Edo kamar hauka

- Kwamishinar da ke kula da harkokin mata da ci gabansu a jihar Edo, Magdalene Ohenhen, tace a yanzu ya zama ruwan dare don uba yayi wa yarsa ciki a jihar

- Ohenhen ta roki mazan jihar da su daina kwana da yayansu mata cewa hakan haramun ne

Kwamishinar da ke kula da harkokin mata da ci gabansu a jihar Edo, Magdalene Ohenhen, tace a yanzu ya zama ruwan dare don uba yayi wa yarsa ciki a jihar.

Ta bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki matuka, cewa ya zama dole a dauki mataki cikin sauri domin da zafi-zafi akan bugi karfe.

Ta yi Magana ne a jiya Laraba, 6 ga watan Fabrairu a Benin lokacin wani zamga-zanga da matasa da mara suka gudanar a jihar karkashin jagorancin Lady Grace Osakue.

Gwamnati ta koka da yadda Iyaye ke yi wa 'Ya 'yan su ciki a Jihar Edo kamar hauka
Gwamnati ta koka da yadda Iyaye ke yi wa 'Ya 'yan su ciki a Jihar Edo kamar hauka
Asali: Depositphotos

Kungiyar na neman a bima wata yarinya yar shekara 17 Gift Alonge hakkinta bayan mahaifinta yayi mata ciki.

Anyi zargin cewa mahaifin yarinyar mai suna Jaco Alonge ya fara yi mata ciki a 2017, sannan kuma ya sake yi mata wani a 2018.

KU KARANTA KUMA: Goyon bayan Atiku babu abunda zai canja a sakamakon zaben Shugaban kasa – Kungiyar Arewa

“Wannan abun akin ciki ne, jihar Edo ya zama abunda ya zama, sannan ya kamata a kawo karshen lamarin cikin gaggawa domin da zafi-zafi akan bugi karfe. Yanzu ya zama ruwan dare yadda maza ke yi wa yayan cikinsu ciki a jihar Edo,”inji kwamishinar.

Ohenhen ta bayyana cewa an samu wani lamari na daban na wani mutum da ke kwana da yar cikinsa tsawon shekaru 10 kafin a kai karan lamarin ga yan sanda.

Tace: “Lokaci yayi da ya kamata mu dakatar da wadannan abubuwan dukka. Jihar Edo ta haramta, haramun ne. Muna rokon mazan Edo da su daina bacci da yayansu mata, haramun ne.”

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel