Arziki-a-gidan-mu: Za'a soma hakar mai a karin wata jihar Arewa - Inji Buhari

Arziki-a-gidan-mu: Za'a soma hakar mai a karin wata jihar Arewa - Inji Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa kamfanin NNPC za ta fara haka mai zurfi domin neman mai da gas a Benue

- Buhari yace za a fara hako man ne biyo bayan wanda aka fara a yankin kogin Kolmani, wanda a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe

- Ya ce a lokacin da yake a matsayin ministan man fetur a shekarun baya, yaga wasu binciken kasa masu ban mamaki, da suka nuna za a iya samun man fetur da gas daga tafkin Chadi ta Benue zuwa yankin Delta

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Laraba, 6 ga watan Fabrairu ya bayyana cewa kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) za ta fara haka mai zurfi domin neman maid a gas a Benue.

Shugaban kasar ya bayyana hakan yayinda yake jawabi ga sarakunan gargajiya a babban dakin taro, gidan gwamnati da ke Maakurdi, babbar birnin jihar Benue.

Yace za a fara hako man ne biyo bayan wanda aka fara a yankin kogin Kolmani, wanda a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

Arziki-a-gidan-mu: Za'a soma hakar mai a karin wata jihar Arewa - Inji Buhari
Arziki-a-gidan-mu: Za'a soma hakar mai a karin wata jihar Arewa - Inji Buhari
Asali: Facebook

Buhari ya tuna cewa a matsayinsa na ministan man fetur a shekarun baya, yaga wasu binciken kasa masu ban mamaki, da suka nuna za a iya samun man fetur da gas daga tafkin Chadi ta Benue zuwa yankin Delta.

Yace yawanci saboda dalilai na kasuwanci yasa anfi zuba hannun jari Niger Delta wanda hakan yasa ake ganin sakamako cikin sauri.

KU KARANTA KUMA: Magoya bayan APC a Bauchi sun sauya sheka zuwa PDP, sun yi bikin kona tsintsiya

Da fari, Tor Tiv ya nuna godiya ga shugaba Buhari kan yadda ya gudanar da kamfen dinsa cikin lumana.

“Mun fuskanci kalubale a 2016, mun gode da ka shiga lamarin, da ka amince da rokonmu na tsaurara matakan tsaro. Operation Whirl Strike yayi nasarar Koran rikicin makiyaya,” inji shi. A nashi jawabin, Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, yayi kira ga zabe na gaskiya da amana inda ya bukaci dukkanin yan takata da su aminta da sakamako.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel