Taba-ka-lashe: Rayuwa, iyali da kuma jerin 'ya'ya da jikokin shugaba Muhammadu Buhari

Taba-ka-lashe: Rayuwa, iyali da kuma jerin 'ya'ya da jikokin shugaba Muhammadu Buhari

Yayin da ya rage saura kwanaki kadan a gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya, akwai bukatar mu kawo maku tarihin rayuwa da kuma iyalan shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da suka hada da 'ya'yan sa da kuma jikokin sa.

Da farko dai shi Shugaba Muhammadu Buhari ya auri matarsa ta farko Safinatu a watan Disambar shekarar 1971.

Yakin basasar Najeriya ya barke ne dan lokaci kadan bayan haduwar Muhammadu Buhari da Safinatu Yusuf, kuma yana daya daga cikin sojojin da aka tura don fafatawa a fagen yakin a bangaren Najeriya.

Taba-ka-lashe: Rayuwa, iyali da kuma jerin 'ya'ya da jikokin shugaba Muhammadu Buhari

Taba-ka-lashe: Rayuwa, iyali da kuma jerin 'ya'ya da jikokin shugaba Muhammadu Buhari
Source: Instagram

KU KARANTA: Hukumar kwastam tayi babban kamu a jihar Legas

Don haka, sai da aka gama yakin a shekarar 1970 aka daura aurensu a watan Disambar 1971.

Hajiya Safina matar Muhammadu Buhari ta farko ta rasu a shekarar 2005 tana da shekara 53 a duniya, sai dai a lokacin da ta rasu ba ta tare da Shugaba Buhari.

Sai kuma matar sa ta biyu kumar uwar gidan sa a halin yanzu wadda suke tare watau Aisha Muhammadu Buhari wadda ya aura bayan sun rabu da matar sa ta farko.

An haifi Aisha ran 17 ga watan Fabrairun 1971 a jihar Adamawa da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kakanta Alhaji Muhammadu Ribadu shi ne ministan tsaron Najeriya na farko.

Jerin sunayen 'ya'yan sa:

1. Sun haifi 'yarsu ta fari da matar sa ta farko watau Zulaiha wacce aka rika kira Magajiya.

Zulaiha ta rasu a shekarar 2012 kuma ta haifi 'ya'ya hudu- Halima (Amira) da Junaid da Muhammadu Buhari da Zulaiha.

Zulaiha ta sha fama da cutar amosanin jini kuma ta rasu ne sakanamon haihuwa.

2. Sai 'yarsu ta biyu Fatima wacce take da yara shidda- Nana Aisha da Khadija da Hauwa da Maryam da Safina da Muhammadu Gidado.

3. Sai dansu na uku kuma shi ne namiji tilo Musa, wanda ya rasu tun yana jariri.

4. Daga shi sai Nana Hadiza wacce take da yara hudu- Amina Amal, da Halima da Mahmoud da Zulaikha.

5. Sannan sai Safina (Lami) wacce ta ke da yara biyu - Isa (Khalifa) da Isma'ila (Fahd).

Sai kuma 'ya'yan da ya haifa da matar sa ta biyu - Aisha Buhari

6. Ta haifi 'yarta ta fari Halima wacce take da diya mace Aisha (Ayush).

7. Sai Yusuf mai bi wa Halima, wanda ya kammala karatunsa a Birtaniya.

8. Sai Zarah Buhari matar wacce take auren Ahmad Indimi dan fitaccen attajirin nan na Najeriya, kuma ta haifi da guda daya Muhammad (Ra'is).

9. Aisha wacce ake kira da Hanaan ce ke bin Zahra.

10. Sannan sai 'yar autar shugaban wato Amina (Noor).

A takaice dai Shugaba Muhammadu Buhari na da 'ya'ya 10 - takwas mata, biyu maza.

Kuma guda biyu a cikin 'ya'yan nasa sun rasu-- Da Zulaiha da Musa.

Shugaban kuma yana da jikoki 18.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel