Bayan shekaru 8, an yanke wa Shugaban NURTW hukuncin kisa kan kashe dan sanda

Bayan shekaru 8, an yanke wa Shugaban NURTW hukuncin kisa kan kashe dan sanda

Wata babbar kotun Ikeja a ranar Talata, 6 ga watan Fabrairu ta yanke hukuncin kisa ga Saheed Arogundade, Shugaban kungiyar ma’ikatan sufuri (NURTW), reshen Boudary/Aiyetoro da ke jihar Lagas, kan kisan wani jami’in dan sanda, Gbenga Oladipupo mai shekara 32.

Kamfanin dillanin labaran Najeriya ta ruwaito cewa Justis Olabisi Akinlade ta saki tare da wanke wasu biyar Mustapha Layeni, Adebayo Abdullahi, Seyi Pabiekun, Sikiru Rufai and Yusuf Arogundade daga tuhuma biyu da ake masu na hada kai dasu wajen aikata kisa da kuma kisan kai.

A shari’an da aka shafe tsawon sa’o’i uku, mai shari’an ta bayyana cewa lauyan mai kara ya tabbatar da cewar Arogundade ne ya kashe dan sandan duba ga irin hujjojin da ya gabatar.

Bayan shekaru 8, an yanke wa Shugaban NURTW hukuncin kisa kan kashe dan sanda

Bayan shekaru 8, an yanke wa Shugaban NURTW hukuncin kisa kan kashe dan sanda
Source: Depositphotos

Kafin ta yanke hukuncin, saboda dalilai na tsaro da kuma guje ma rikici a yayin ci gaba da shari’an, mai shari’a ya yi umurnin cewa a kulle kofar dakin kotun, sannan aka mika mata makullin.

Daga nan sai ta yanke masa hukuncin kisan kai ta hanyar rataya har sai ya mutu.

KU KARANTA KUMA: PDP ta samu karin magoya baya 10,000 a jihar Bauchi

A lokacin da ya ji hukuncin da aka yanke masa, sai Arogundade ya fadi warwas a kasa yayinda yan uwansa ke ta gurnani da koke-koke a kotu.

A tattaro cewa Misis C. Rotimi-Odutola, mai laifin ya aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Afrilu 2010, a mararrabar Gbara, Ajegunle, Lagas.

A cewarta an kashe Oladipupo ne saboda yana yawan karfafa gwiwar amfani da adaidaita sahu a Aiyetoro wanda hakan ke janyo rashin ciniki ga kungiyar NURTW.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel