Ba uwa ba riba komawarka PDP - Ganduje ya soki Kwankwaso kan fita daga APC

Ba uwa ba riba komawarka PDP - Ganduje ya soki Kwankwaso kan fita daga APC

- Gwamnan Ganduje ya ce Kwamkwaso, ya bar jam'iyyar APC domin samun tikitin takarar kujerar shugaban kasar, sai dai ya yi biyu babu ko daya

- Gwamnan ya yi nuni da cewa siyasar Kano ta Buhari ce, kuma Buhari ne siyasar Kano

- Ya ce jam'iyyar APC a Kano ba ta fuskantar wata baraka, saboda an gudanar da zabukan fitar da gwani cikin nasara ba tare da korafe korafe ba

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a ranar 5 ga watan Fabreru, ya ce wanda ya gaji shugabancin jihar a wajensa, Rabiu Musa Kwamkwaso, ya bar jam'iyyar APC cikin gaggawar samun tikitin takarar kujerar shugaban kasar, sai dai ya yi biyu babu ko daya.

Ganduje, wanda ya yi jawabi a yayin da ya karbi bakunci kwamitin tuntuba na yakin zaben shugaban kasa Buhari da ke cikin kungiyar yakin zabensa a gidan gwamnatin jihar, ya ce Kwankwaso ya manta da cewa tuni kujerar shugaban kasar da ya ke hari wani ya riga shi, babu matsugunninsa a wajen.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Dogara ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, ya kira shi Fir'auna

Ba uwa ba riba komawarka PDP - Ganduje ya soki Kwankwaso kan fita daga APC

Ba uwa ba riba komawarka PDP - Ganduje ya soki Kwankwaso kan fita daga APC
Source: Original

Ya ce: "Kwankwaso ya nemi mukamin da bai wanzu ba a APC shi ya sa ya fice daga jam'iyyar bayan gane hakan; sai dai can ma da ya je PDP ya sha kasa, wanda ya sanya shi ya yi batan bakatantan, ba dayan kanwar biyu."

Gwamnan ya yi nuni da cewa: "Siyasar Kano ta Buhari ce, kuma Buhari ne siyasar Kano, a yau Kano ta APC ce kuma jama'a na tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma babu wani abu da wani mutum zai iya yi akan hakan."

Ya ce jam'iyyar APC a Kano ba ta fuskantar wata baraka, saboda an gudanar da zabukan fitar da gwani cikin nasara ba tare da korafe korafe ba, "kuma a yau mambobi 30 cikin 40 na majalisar dokokin jihar na takara ba tare da fuskantar wata matsala ba, kuma sanatoci 2 cikin 3 za su koma ba tare da wata matsala ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel