Amurka ta rude: Kasar Iran tayi gwajin wasu manyyan makaman ta masu linzami

Amurka ta rude: Kasar Iran tayi gwajin wasu manyyan makaman ta masu linzami

Kasar Iran dake a yankin gabas ta tsakiya ta sanar da samun nasarar yin gwajin makaman ta masu linzamin da ta kera wadanda ka iya yin tafiyar sama mai nisan da ya wuce kilomita dubu 1 da dari 350 a sararin samaniya zuwa wajen abokan gaba.

Shi dai wannan gwajin na sabon makamakin na Iran ya zo a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da bukukuwan cika shekaru 40, da kafuwar Jamhuriyar Musulunci tun bayan juyin juya halin da suka gudanar a shekarar 1979 da ta gabata.

Amurka ta rude: Kasar Iran tayi gwani wasu manyyan makaman ta masu linzami

Amurka ta rude: Kasar Iran tayi gwani wasu manyyan makaman ta masu linzami
Source: UGC

KU KARANTA: Buhari ko Atiku: Zakzaky ya fadawa mabiyan sa yadda za suyi a zaben 2019

Legit.ng Hausa ta samu cewa sanarwar wadda ta fito daga bakin Ministan tsaron kasar ta Iran Amir Hatami, ta bayyana cewa an gudanar da gwajin makamin mai linzamin ne daga tazarar kilomita dubu 1 da 200, kuma yayi nasarar kaiwa inda aka saita shi.

Idan mai karatu bai manta ba, a shekarar 2015 kasar ta Iran ta cimma yarjejeniyar dakatar da shirye-shiryenta na inganta makamashin nukilya tsakaninta da manyan kasashen duniya.

Sai dai kuma sakasar ta ci gaba da kera manyan makamai masu linzami, daya daga cikin matakan da yasa Amurka ficewa daga yarjejeniyar ta 2015 a watan Mayu na shekarar bara, tare da kakaba mata takunkuman karya tattalin arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel