Lafiya: Amfani da Tumatir gwalgwaji na janyo cutar daji - Masana

Lafiya: Amfani da Tumatir gwalgwaji na janyo cutar daji - Masana

Wata masaniyar kiwon lafiyan abinci, Toyin Aliu, ta kwalegin fasahar kiwon lafiya da ke karamar hukumar Offa, jihar Kwara, ta bayyana cewa amfani da tumatur rubabbe wanda aka fi sani da gwalgwaji na janyo cutar daji.

Mrs Aliu ya bayyanawa manema labarai a hiran wayan tarho ranan Talata a garin Offa cewa tsutsotsin da ke cikin tumaturin na zama cututtuka idan aka ci.

Tace: "Tsutsan da ke cikin tumatir rubabbe ke kawo kwayar cutar mycotoxins wanda ke da hadari ga lafiyan dan adam."

"TumatiR gwalgwaji na iya kara yiwuwan cutar daji, saboda idan tumatir ya rube, wasu tsutsotsi na shiga da ido ba zai gani ba."

"Tunda tumatir na da ruwa da yawa cikinsa, kwayar cutar mycotoxins kan nutse cikinsa sannan ya bata dukkan tumaturin wanda zai zamo hadari ga jiki."

Lafiya: Amfani da Tumatir gwalgwaji na janyo cutar daji - Masana

Lafiya: Amfani da Tumatir gwalgwaji na janyo cutar daji - Masana
Source: Original

KU KARANTA: Jerin sunayen kamfanoni 6 da zasu gina hanyoyi 19 a fadin tarayya, Dangote ne na daya

Ta kara da cewa duk da gwalgwaji ya fi arha a kasuwa, abinda yafi kyau shine sayan masu tsadan saboda rana goben lafiyan jikin dan Adam.

A cewarta: "Illan amfani da irin wadannan tumaturin ba farar daya bane, kadan-kadan zai rika cin jikin mutum. Saboda haka, gwamma mutum yaci mai tsada da wanda ya sanya shi nadama gobe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel