Da yawa sun jikkata a rikicin da ya barke tsakanin masoyan APC da PDP a Delta

Da yawa sun jikkata a rikicin da ya barke tsakanin masoyan APC da PDP a Delta

- Rahotanni na nuni da cewa rikicin siyasa ya barke tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Delta

- Rikicin dai da ya barke tsakanin jam'iyyun biyu ya faru ne a wurare mabanbanta, a kananan hukumomin Uwie da Ethiope ta Gabas

- Wani da rikicin ya faru a gabansa, ya ce akalla mutane 20 ne suka jikkata sakamakon sara da makamai ko harbi da bindiga a lokacin rikicin da ya faru

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu daga shafin talabijin na Channels, na nuni da cewa rikicin siyasa ya barke tsakanin magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da jam'iyyar adawa ta the Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Delta.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Delta, Andrew Aniamaka, ya tabbatar da faduwar rikicin a zantawarsa da gidan talabijin na Channels a ranar Litinin a garin Asaba, babban birnin jihar.

A cewarsa, an samu rikicin ne tsakanin magoya bayan jam'iyyun biyu a wurare mabanbanta, daya a karamar hukumar Uwie sai kuma daya a karamar hukumar Ethiope ta Gabas.

KARANTA WANNAN: Ku yi ku gama: Karewar wa'adin mulkina ba shi ne karshen siyasata ba - Gwamnan Imo

Da yawa sun jikkata a rikicin da ya barke tsakanin masoyan APC da PDP a Delta

Da yawa sun jikkata a rikicin da ya barke tsakanin masoyan APC da PDP a Delta
Source: UGC

Aniamaka ya kara da cewa rikicin ya yi sanadin jikkatar wasu da dama, wanda kuma ya faru kasa da makwanni biyu da gudanar da babban zabe na kasar.

Haka zalika, ya tabbatar da cewa rikicin wanda ya barke a garin Abraka tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da PDP, ya kuma yi nuni da cewa jami'an tsaro sun isa wajen da lamarin ya faru cikin gaggawa inda suka kwantar da tarzoma.

A wani labarin kuwa, wanda rikicin ya faru a gabansa, ya ce akalla mutane 20 ne suka jikkata sakamakon sara makamai ko harbi da bingiga a lokacin rikicin da ya faru tsakanin ranar Juma'a zuwa ranar Litinin a yankin.

Ya kuma yi ikirarin cewa akalla mutane 3 ne aka kashe a yayin da 'yan bangar siyasar bangarorin jam'iyyun biyu suka fara musayar harsasai a tsakaninsu, wanda ba zai rasa nasaba da babban zabe mai zuwa ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel