Assha: Tsohon DCG hukumar kwastan ya gamu da ajalinsa a hannun 'yan bindiga

Assha: Tsohon DCG hukumar kwastan ya gamu da ajalinsa a hannun 'yan bindiga

- Yan bindiga sun kashe tsohon mataimakin babban konturolan hukumar da ke yaki da fasa kwabri ta kasa, Dr Adewale Oloyede (mai ritaya) a jihar Kogi

- Yan bidigar sun kashe tsohon mataimakin shugaban hukumar na kasar tare da mai tsaronsa Dauda Yusuf nMichael a ranar Juma'a

- Kafin mutuwarsa, Oloyede na daya daga cikin mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki na kasa kan bunkasa gidajen yaji da rage cin koso

Rahoton da muke samu yanzu na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne, sun kashe tsohon mataimakin babban konturolan hukumar da ke yaki da fasa kwabri ta kasa, Dr Adewale Oloyede (mai ritaya) tare da mai tsaronsa, Dauda Yusuf Michael, wani babban sifeta na hukumar a garin Osara, jihar Kogi.

Mai magana da yawun hukumar hana fasa kwabri ta kasa, kwastan, DCP Francis Enobore, ya sanarwa jaridar Vanguard na ranar Litinin a Abuja cewa tsohon jami'in hukumar na kan hanyarsa ta zuwa Legas a cikin motarsa a lokacin da 'yan ta'addar suka far masa da misalin karfe 3 na ranar Juma'a.

KARANTA WANNAN: Yakin zabe: Mun kammala babban shiri kan zuwan Buhari garin Lafiya - Yan sanda

Assha: Tsohon DCG hukumar kwastan ya gamu da ajalinsa a hannun 'yan bindiga
Assha: Tsohon DCG hukumar kwastan ya gamu da ajalinsa a hannun 'yan bindiga
Asali: Twitter

Ya ce: "Kafin kisan tsohon babban jami'in hukumar, ya kasance likita, mai kula da sashen lafiya da walwalar ma'aikata na hukumar na tsawon shekaru kafin ajiye aikinsa a shekarar 2007.

"Kafin mutuwarsa, Oloyede na daya daga cikin mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki na kasa kan bunkasa gidajen yaji da rage cin koso karkashin shugabancin babban jojin gwamnatin tarayya, mai shari'a Ishaq Bello.

"A yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da bincike, ya kyautu a garemu mu yi addu'ar cewa Allah ya tona asirin wadanda suka yi wannan aika aikar, domin yi masu hukunci dai-dai da laifin da suka aikata."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel