Yakin zabe: Mun kammala babban shiri kan zuwan Buhari garin Lafiya - Yan sanda

Yakin zabe: Mun kammala babban shiri kan zuwan Buhari garin Lafiya - Yan sanda

- Rundunar 'yan sanda ta ce ta kammala shirin raba jami'anta 2,000 domin samar da tsaro a lokacin da Buhari zai je kaddamar da yakin zabensa a garin Lafiya

- ASP Samaila Usman, ya ce manufar hakan shine, tabbatar da cewan yakin zaben ya kammala ba tare da hatsaniya ko rikici ba

- Usman ya kuma kara da cewa rundunar za ta rufe wasu tituna na cikin garin Lafia a lokacin yakin zaben shugaban kasar

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Nasarawa ta ce ta kammala shirin raba jami'anta 2,000 domin samar da kyakkyawan tsaro a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai je kaddamar da yakin zabensa a ranar Laraba, a garin Lafiya.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Samaila Usman, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a ranar Talata a garin Lafiya cewa manufar hakan shine, tabbatar da cewan yakin zaben ya kammala ba tare da hatsaniya ko rikici ba.

Usman ya ce an zakulo jami'an ne daga sashen jami'an sintiri (PMF), sashen dakile ta'addanci da kuma sashen kwararru.

KARANTA WANNAN: Ana wata ga wata: Obasanjo ya kaddamar da yakin zaben Buhari a Amurka

Rundunar 'yan sanda ta yi wani babban shirin kan yakin zaben Buhari a Lafia
Rundunar 'yan sanda ta yi wani babban shirin kan yakin zaben Buhari a Lafia
Asali: Facebook

A cewar sa, kwamishinan 'yan sanda na jihar, Adebola Emmanuel-Longe, ya kuma tura jami'ai na musamman daga sashen lalata ababen fashewa, da kuma sauran jami'an rundunar zuwa lungu da sako na yankin da shugaban kasar zai kaddamar da yakin zaben na sa.

Usman ya kuma kara da cewa rundunar za ta rufe wasu tituna na cikin garin Lafia a lokacin yakin zaben shugaban kasar, inda ya bukaci al'ummar jihar da su baiwa rundunar hadin kai a lokacin yakin zabensa da kuma bayan kammala shi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel