Allah-mai-iko: An tono kaburburan wasu kamar yadda aka binne su bayan shekaru a Misira

Allah-mai-iko: An tono kaburburan wasu kamar yadda aka binne su bayan shekaru a Misira

Labarin da muka samu daga majiyar mu ta TRT ta bayyana mana cewa mahukunta sun samu zarafin tono wasu kaburbura uku da gawarwakin mutane 40 a wata makabarta a garin Minye dake kasar Misira.

Kamar dai yadda Ministan harkokin tarihin kasar Masar Halid el-Anani ya bayyanawa manema labarai a Alkahira babban birnin kasar Masar, ya bayyana cewar an tonu wasu kabubbura da aka ga gawarwaki 40 da suka hada da yara 10 kamar yadda aka binnesu a yankin Tuna dake karkashin birnin Minye.

Allah-mai-iko: An tono kaburburan wasu kamar yadda aka binne su bayan shekaru a Misira

Allah-mai-iko: An tono kaburburan wasu kamar yadda aka binne su bayan shekaru a Misira
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wata mata ta damfari Dangote

Legit.ng Hausa ta samu cewa hukumar kula da kayan tarihi ta bayyana cewar za'a iya gano wasu kabubbura guda uku, an kuma yi kabuburan da duwatsu kamar yadda Anani ya bayyana.

Gawarwakin da aka ganon an bayyana cewar wasunsu su a sanya su cikin makarar duwatsu, katako wasu kuwa an rufe su ne ba tare da makara ba. Ba'a dai bayyana wadannan gawarwakin ko na wasu lokutta bane.

A wani labarin kuma, A yayin da zabukan gama gari na shugaban kasa, 'yan majalisar tarayya da kuma gwamnoni da 'yan majalisar jahohi ke cigaba da karatowa, yanayin siyasar na cigaba da zafafa tare da daukar sabon salo kala-kala, 'yan siyasa na cigaba da bayyana ra'ayoyin su.

A yayin da ake cikin hakan ne muka samu labarin cewa dan takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara a daya daga cikin jam'iyyun adawa ta All Progressives Grand Alliance (APGA) mai suna Alhaji Sani Shinkafi yace mabiyan sa su zabi shugaba Muhammadu Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel